fidelitybank

Amurka ta kuduri niyar inganta shirye-shiryen kafafen yada labarai a Najeriya

Date:

Gwamnatin kasar Amurka ta ce kudurin ta na aniyar tallafawa shirye-shiryen da ke inganta da ilimin kafafen yada labarai.

Da ya ke jawabi a wajen bikin bude taron bitar a jihar Legas a ranar Litinin, jami’in hulda da jama’a na ofishin jakadancin Amurka, Stephen Ibelli ya bayyana cewa, ingantacciyar dimokuradiyya na bukatar dukkanin jama’a da a ka sa ni da kuma kafafen yada labarai masu kishin kasa wadanda ke ba da bayanai na gaskiya da gaskiya.

Shirin dai tare da goyon bayan Babban Ofishin Jakadancin Amurka a Legas da  Cibiyar yada labarai ta Afirka ta Yamma (WABMA) da Enugu Literacy Society (ELS), sun kaddamar da shirn na “Project Fact Check Nigeria,” wani aikin jarida da kuma magance rashin fahimta na zakulo bayanan gaskiya.

Aikin ya na neman ƙarfafa dabarun tunani, faɗaɗa ilimin zamani na dijital da kafofin yada labarai da haɓaka ƙarfin ƴan jaridun rediyo, domin magance munanan labarai da na ɓarna a jahohi 17 na kudancin Najeriya.

Sama da masu yada shirye-shiryen rediyo 170, ciki harda furodusoshi, da masu ba da rahoto za su sami ƙwarewar bincikar gaskiya da na mafi kyawun ayyuka, domin kaucewa yada labaran kanzon Kurege da kuma rashin fahimta.

“Ta hanyar inganta ilimin kafofin yada labarai, mu na ƙarfafa ka’idodin gaskiya, shugabanci nagari da kuma bin doka da ke aiki a matsayin ginshiƙan tsarin dimokuradiyyar mu,” inji Ibelli.

 

nhgsfp

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...

A sake sabon tsarin shugabancin INEC a Najeriya – Goodluck

Tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan, ya yi kira da...

Magoya bayan West Ham ku hada kai da Bowen – Potter

Mai horas da West Ham, Graham Potter ya bukaci...

Alhaki na ne kifewar jirgin kasa – Shugaban Hukumar

Shugaban hukumar jiragen ƙasa ta Najeriya (NRC), Kayode Opeifa,...

Tinubu ya haramta fitar da ɗanyen man kaɗanya

Shugaban kasa, Bola Tinubu, ya bayar da umarnin dakatar...

Hisba ta karɓi ƙorafe-ƙorafe 83,776 a Kano

Rundunar Hisbah ta jihar Kano ta bayyana cewa, a...

Ganduje ba dan cin hanci ba ne – Martanin Garba Ga Gwamnatin Kano

Tsohon kwamishinan yaɗa labarai na Jihar Kano, Muhammad Garba,...

Kungiyar Malaman Jami’o’i bangaren BUK sun yi zanga-zangar Lumana

Kungiyar Malaman Jami’o’i (ASUU), reshen Jami’ar Bayero Kano (BUK),...
X whatsapp