fidelitybank

Amurka ce za ta ji jiki idan za mu yi fadan kasuwanci – China

Date:

Ma’aikatar lafiyar China ta bayyana cewa za ta kare “muradun ƙasarta” bayan Shugaban Ƙasar Amurka Donald Trump ya bayyana wa manema labarai cewa yana tunanin sanya harajin kashi 10 a kan dukkan kayayyakin China.

“Mun yi amannar cewa babu ƙasar da za ta ci riba idan ana jayayya da rikici kan kasuwanci ko musayar ƙaƙaba haraji,” in ji kakakin ma’aikatar, Mao Ning.

Ta ƙara da cewa “China za ta yi duk mai yiwuwa domin kare muradunta,” in ji ta.

Trump ya ce zai yiwu harajin da zai ƙaƙaba ɗin ya fara aiki daga 1 ga Fabrairu, kuma saboda China tana tura fentanyl zuwa ƙasar Mexico da Canada ne, duk da cewa China ta sha musanta zargin a baya safarar miyagun ƙwayoyi a baya.

Trump ya kuma ce zai ƙaƙaba harajin shigo da kayayyaki daga Canada da Mexico. In ji BBC.

current eggon news

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Fernandes na duba yiwuwar barin Man Utd zuwa Al-Hilal

Bruno Fernandes na duba yiwuwar ficewa daga Manchester United...

Gwamnatin Tinubu ta jefa al’umma fiye da miliyan 150 cikin tsananin talauci – NLC

A daidai lokacin da gwamnatin shugaban Najeriya Bola Ahmed...

Sojoji sun ce sun hallaka ƴan Ta’adda 60 a jihar Borno

Dakarun sojijin Operation Haɗin-Kai sun ce sun kashe ƴan...

Zan cigaba da jajircewa a kan rantsuwar da na yi ta kujera ta – Fubara

Gwamnan jihar Ribas da aka dakatar, Sim Fubara, ya...

Ambaliya ya kashe Mutane a jihar Neja

Wasu rahotanni sun bayyana cewa, mutane da dama sun...

Kotu ta tabbatar da nasarar Gwamnan Edo

Kotun daukaka kara da ke Abuja ta amince da...

An kashe aƙalla mutum 10,217 a mulkin Tinubu – Amnesty

Wani bincike da ƙungiyar Amnesty International ta fitar kwanan...

Gwamnati ba ta tausayin Talaka – Atiku

Ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar PDP a zaben...

Elon Musk ya ajiye aikin da Trump ya naɗa shi

Hamshaƙin attajirin nan Elon Musk ya sanarda aniyarsa ta...

‘Yar Najeriya ta haihuwa a aikin Hajjin bana

Wata mata da ta je aikin hajji daga jihar...

Rashin nadi da jinkiri ne ya kawo rashin nasarar mu a kakar 2024/2025 – Kano Pillars

Kungiyar Kano Pillars ta yi imanin cewa jinkirin shirye-shiryen...
X whatsapp