fidelitybank

Ministan makamashi ya gaggauta sauka daga mukaminsa saboda katsewar lantarki – NLC

Date:

Ƙungiyar ƙwadago ta Najeriya, ta yi kira ga Ministan Makamashi, Adebayo Adelabu da ya sauka saboda yawaitar katsewar babban layin lantarki na ƙasa.

A wata sanarwa da shugaban ƙungiyar, Joe Ajaero ya fitar, ya ce ƙungiyar na takaicin yadda ɓangaren lantarkin Najeriya ya ƙi gyaruwa, kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito.

Ajaero ya ce, “idan har akwai ma’aikata ƙwararru waɗanda suka san makamai aiki a ma’aikatar makamashi, to lallai za a iya kiyaye yawaitar abin kunyar nan da ake fuskanta na yawaitar katsewar layin lantarki a Najeriya. Magance matsalar ya kamata ministan ya yi, ba tiƙa maganar cewa za su magance ta ba.

“Mun yi amannar cewa wannan na nuna rashin ƙwarewa da gazawar ma’aikatar makamashin, wanda hakan ya sa muke mamakin me ya sa wanda ke jagorantar ma’aikatar ba zai sauka cikin mutunci ba.”

Ajaero ya kuma caccaki ministan bisa kasafta kashe naira biliyan 8 a kasafin kuɗin 2025 domin “wayar da kan ƴan Najeriya muhimmancin biyan kuɗin lantarki.”

besda salary

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Mu na aiki tuƙuru wajen daƙile ayyukan ta’adda a Najeriya – Christopher Musa

Babban hafsan tsaron Najeriya, Janar Christopher Musa, ya tabbatarwa...

Mayaƙan ISWAP sun harbe Manoma 23 a Borno

Rahotanni sun bayyana cewa ƙungiyar mayaƙan ISWAP ta kashe...

Real Madrid ta ɗauki ɗan wasan baya daga Bournemouth

Real Madrid ta sanar da sayen ɗan wasan baya...

Gwamnatin Kano ta haramta yin bikin Ƙauyawa da gidajen biki

Hukumar tace fina-finai a jihar Kano ta sanar da...

An kashe ƴan Boko Haram biyar a Borno

Dakarun sojin Najeriya haɗe da wasu maharba sun daƙile...

Farashin Shinkafa zai cigaba da sauka – BUA

Shugaban rukunin kamfanonin BUA, Abdul Samad Rabiu, ya alƙawarta...

An kashe mutane 10 a wani sabon rikici da ya ɓarke a Filato

Aƙalla mutabe 10 ne aka kashe tare da sace...

Duk da sauƙin da aka samu har yanzu Abuja na fuskantar hauhawar farashi

Duk da cewa hukumar ƙididdiga ta ƙasa NBS, ta...

Hauhawar farashi ya ragu da kaso 23.71 a Najeriya – NBS

An samu raguwar hauhawar farashin kayayyaki a Najeriya daga...

Fiye da mutane 100 Makiyaya aka kashe a Jos

An ruwaito cewa an kashe wani makiyayi guda da...

Tinubu ka kori shugaban JAMB – Sowore

Dan siyasa mai fafutuka, Omoyele Sowore, ya yi kira...

Majalisa ta yi watsi da ƙudirin karɓa-karɓa

Majalisar wakilai ta yi watsi da wani ƙudirin doka...
X whatsapp