Jamiāan tsaro na Amotekun na jihar Ekiti sun kama mutane bakwai da suka hada da mata biyu, bisa zargin laifuka daban-daban kamar fashi da makami.
Da yake magana da manema labarai a Ado Ekiti, kwamandan Amotekun a jihar Ekiti, Mista Joe Komolafe ya bayyana cewa an kama wadanda ake zargin ne a Ara, Aisegba, da Ado Ekiti.
Mista Komolafe ya ce an kama wadanda ake zargin ne biyo bayan wani rahoto da wasu alāummar yankin suka samu.
Shugaban na Ekiti Amotekun ya bayyana cewa biyu daga cikinsu sun kware wajen yin fashin motoci a kan hanyar Iluomoba- Aisegba, yayin da sauran hudun suka kware wajen kwace babura.
Kwamandan wanda ya ce za a mika wadanda ake zargin ga jamiāan tsaro domin gurfanar da su a gaban kuliya, ya ce biyu daga cikinsu tsoffin da aka yanke wa hukunci ne.
Mista Komolafe ya yi kira ga mazauna jihar da su kai rahoto ga jamiāan tsaro domin daukar matakin gaggawa.
A yayin tattaunawar, wadanda ake zargin sun yarda cewa sun aikata laifin.
Kayayyakin da aka kwato daga hannunsu sun hada da babura hudu, wayoyi 16, abin rufe fuska, wukake, injin fanfo ruwa, da dai sauransu.