fidelitybank

Amnesty ta naɗa tsohon Ɗan Jarida a matsayin daraktan ta a Najeriya

Date:

Ƙungiyar kare hakkin ɗan’adam ta duniya Amnesty International, ta sanar da naɗa Isa Sanusi, mai fafutukar kare haƙƙin dan’adam kuma tsohon dan jarida a matsayin sabon daraktanta na Najeriya.

Wata sanarwa da shugaban kwamitin amintattu na Amnesty International a Najeriya, Auwal Musa Rafsanjani ya fitar, ta ce Isa Sanusi zai jagoranci fadada ayyukan bincike da gangamin kungiyar a Najeriya.

Zai kuma mayar da hankali a kan al’amuran da suka shafi rikice-rikice da ilmi da kare hakkin dan’adam da daidaiton jinsi da sauyin yanayi da shigar da matasa cikin harkokin ingantawa da kare hakkin dan’adam.

“Nadin Isa Sanusi a matsayin daraktan kasa zai karfafa tasirin kungiyar Amnesty International a Najeriya.

Yana da gogewar aiki ta tsawon shekara bakwai, abin da ke nufin zai ba da gudummawa wajen ci gaba da ganin tasirin ayyukan Amnesty a Najeriya,” in ji Auwal Musa Rafsanjani.

Kafin sabon nadin nasa, Isa Sanusi shi ne manajan yaɗa labarai da sadarwa na Amnesty International a Najeriya, mukamin da yake rike da shi tun 2016. Ya kuma taɓa aikin jarida da BBC tsawon shekara 10, sannan ya taɓa zama mataimakin editan jaridar Daily Trust.

Mallam Isa ya kuma jagoranci ayyukan kare hakkin dan’adam iri daban-daban da horar da masu fafutukar kare hakkin dan’adam a Najeriya.

Ya yi digirin farko a fannin Ingilishi a Jami’ar Bayero Kano sannan yana da digiri na biyu a fannin aikin jarida daga Jami’ar Landan.

sspdf news today

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Da yuwar Sojojin mu za su shiga yaƙi don tallafa wa Isra’ila – Trump

Rundunar sojin Isra'ila IDF ta ce ta ƙaddamar da...

Isra’ila ta kai hari cibiyoyin ƙera nukiliyar Iran

Yayin da aka shiga rana ta shida na yaƙi...

Najeriya za ta kwashe ƴan ƙasarta dake zaune a Iran da Isra’ila

Gwamnatin tarayya ta ce, tana kammala shirye-shiryen gaggawa domin...

Makami mai Linzami ya faɗa kan cibiyar tattara bayanan sirrin Isra’ila

Kafar yaɗa labarai ta gwamnatin Iran ta ce, ƙasar...

Iran ta ƙaddamar da sabbin hare-haren makamai masu linzami kan Isra’ila

Rundunar sojin Isra'ila ta ce, Iran ta ƙaddamar da...

Isra’ila ta na da makaman nukiliya 90

Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu ya dade yana cewa Iran...

Kashe jagoran Iran Ayatullah shi ne kawo ƙarshen rikici – Isra’ila

Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu ya ce duk wani shiri...

Jerin sunayen masu Fashin Waya 51 da aka kama a Kano

Rundunar ƴansandan Kano, ta fitar da jerin sunayen Mutane...

Iran ta dakatar da tashin jirgi a ƙasarta

Hukumar kula da zirga-zirgar jiragen sama ta Iran ta...

Poland za ta kwashe dukkannin ƴan ƙasarta daga Isra’ila

Poland na shirin kwashe kusan ‘yan kasarta 200 daga...

Kisan Binuwai abun haushi ne bai kamata a ƙyale ba – Atiku

Atiku Abubakar ya yi Allah-wadai da Kisan Benue, tare...

Ƴan Bindiga sun ajiye makamai a Katsina

Wasu fitattun jagororin ƴanbindiga da suka addabi yankunan ƙaramar...
X whatsapp