Hukumar agajin gaggawa ta NEMA, ta ce, ambaliyar ruwa ta lalata yankuna 225 sakamakon ruwan sama mai karfin gaske da ake tafkawa a kananan hukumomi 31 da ke Kano da Jigawa tun daga watan Yuli zuwa yanzu.
Dakta Nuradeen Abdullahi, na hukumar ta NEMA da ke kula da Kano da Jigawa a lokacin wannan sanarwa ya ce wannan yanayi ya tilastawa mutane da dama rasa matsugunaio da hijira zuwa wasu yankunan.
Kananan hukumomin da ambaliyar ta shafa a Kano sun hada da Tudun Wada; Doguwa, Kibiya, Kiru, Gwale, Danbatta, Bagwai, Ajingi, Albasu, Shanono, Tsanyawa, Rimin Gado and Dawakin Kudu.
A Jigawa kuma akwai kananan hukumomi irinsu, Kafin hausa; Malam madori, Hadejia, Guri, Auyo, Birniwa, Jahun, Miga, Kiyawa, Birnin Kudu, Kaugama, Babura, Gwaram, Dutse da Kirikasamma.
Abdullahi ya ce ambaliya ta lalata gidaje da gine-gine da gonaki da wajen kiwo da sauran tarin dukiyoyi.,
Akwai daruruwa kuma da ba su da makwanci.


