Dubban mutane sun hau kan titunan birnin Ibdan na jihar Oyo, domin nuna fushin su kan tsadar rayuwa a Najeriya.
Zanga-zangar ta fara ne daga yankin Mokola ta birnin, inda masu yin tattakin suka yi mahaÉ—a.
Hakan na zuwa ne bayan gudanar da irin wannan zanga-zanga a jihohin Kano da Neja, inda mutane da dama suka fito domin kokawa kan matsalar tashin farashin kayan masarufi.
Al’umma a Najeriya na fama da matsalar tashin kayan masarufi ne tun bayan da shugaban Æ™asar, Bola Tinubu ya ayyana cire tallafin man fetur a ranar 29 ga watan Mayun 2023, jim kaÉ—an bayan ratsar da shi a matsayin shugaban Æ™asa.
Tun daga wancan lokacin ne farashin wasu kayan masarufi da abinci da sufuri suka nunka, lamarin da ya Æ™ara jefa al’ummar Æ™asar cikin mawuyacin hali.
Tun farko rundunar Æ´ansandan Najeriya a jihar Oyo ta gargaÉ—i masu zanga-zangar da su kauce wa duk wani abu da zai tayar da hankalin al’umma kuma ta bayyana cewa za ta tsaurara tsaro domin ganin lamarin bai rikiÉ—e zuwa tarzoma ba.
Gwamnatin Najeriya dai ta bayyana cewa tana yin duk abin da ya kamata wajen sauÆ™aÆ™a wa al’umma halin matsin na rayuwa, inda ta ayyana wani shiri na tallafin kayan abinci da na masarufi ga al’umma.


