fidelitybank

Aikin NDLE ya yi kamanceceniya da aikin musulunci – JIT

Date:

Ƙungiyar Jama’atut Tajdidil Islam, JTI, Reshen Jihar Kano, ta ce aikin Hukumar Hana Sha Da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi ta Najeriya, NDLEA, ya yi daidai da tsarin addinin Musulunci.

Jami’in Huɗɗa da Jama’a na JTI ta Kano, Muhammad Albakary ne ya bayyana haka ne ranar Litinin a jihar Jigawa lokacin da suka kai wata ziyarar aiki ga hukumar NDLEA reshen jihar.

Al-Bakariy ya ce aikin NDLEA ya dace tsarin addinin Musulunci na hani da mu’amala da dukkan kayen maye domin kiyaye hankali da mutunci da addini.

Da ya ke mayar da jawabi, Shugaban NDLEA ta Jigawa, Ibrahim Buraje ya ce asalin kundin hukumar da aka rubuta kacokan ya bayyana tsarin addini ne na tabbatar da cewa saya da sayarwa da sha da fataucin miyagun ƙwayoyi haramun ne a tsarin wannan hukuma.

Ya kuma bayyana ƙudirin hukumar na aiki hannu da hannu da JTI.

Jami’an da suka zamu zuwa ziyarar aikin sun haɗa da Isma’il Kudai wanda shi ne Shugaban Kungiyar JTI na Jihar Jigawa, Nuru Adam Galadanci, Ibrahim Rabi’u Fagge, Muhammad Zangina Kura, Umar Isma’il Ajingi, Umar Shehu Tsakuwa, Sharif Muhammad Hamza da Aliyu Ibrahim Sani Mainagge.

 

nigeria legit news

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp