Hukumar ƙidaya ta Najeriya ta ce yaran da aka haifa 424,302 ta yi wa rijista a cikin jihar Gombe, tsakanin watan Janairu zuwa Nuwamba.
Daga cikin jariran da aka yi wa rijistar haihuwar, 187,283 ko kashi 44.13 mata ne, yayin da maza suka kasance 237,019 ko kuma kashi 55.86.
Jaridar Punch ta ruwaito shugaban sashen yin rijista da tattara muhimman alƙaluma na hukumar ƙidaya ta ƙasa reshen jihar Gombe Mista Adedeji Adeniyi lokacin da yake bayar da ƙarin bayani kan alƙaluman yau Juma’a a jihar Gombe.
Ya ce an yi rijistar haihuwar ce a cibiyoyi fiye da 100 na jihar kuma an yi ƙananan yara daga kan jarirai sabbin haihuwa har zuwa ‘yan shekara 17.
Mista Adedeji Adeniyi ya ce mutum 76,900 na waɗanda aka yi wa rijistar ƙananan yara ‘yan ƙasa da shekara ɗaya, kuma ya ce 33,760 daga cikinsu mata ne sai maza kuma 43,140.


