Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC), ta bayyana damuwarta kan yadda mazauna yankin jiharĀ Katsina suka yi rijistar katin zabe na dindindin (PVC) a sabbin rumfunan zabe 1,750 da aka kafa a jihar.
Alhaji Jibril Zarewa, kwamishinan zabe na INEC a jihar, ya bayyana hakan a wata hira da kamfanin dillancin labarai na kasa NAN a ranar Jumaāa a Katsina.
Ya ce, bayan shekara daya da fara rajistar PVC, an samu rashin fitowar jamaāa domin yin rajista a sabbin rumfunan zabe da aka kafa.
A cewar Zarewa, āA watan Mayun 2022 da muka yi bincike, mun gano a cikin sabbin rumfunan zabe 1,750 da aka kafa, kusan guda 1,200 ba su da mutane sama da 50 da suka yi rajista a kowannen su.
āWannan rijistar ta Ęunshi canja wuri. Wasu rumfunan zabe ba su da rijista, wasu na da guda daya, wasu biyar yayin da wasu ba su wuce mutane 50 da suka yi rajista ba.
āKo da yake ana iya danganta hakan da dakatar da hanyoyin sadarwa a kananan hukumomi 17 daga cikin 34 na kananan hukumomi kusan watanni biyar saboda matsalar tsaro.
āMuna kira ga alāummar yankunan da aka kirkiro sabbin rumfunan zabe da su je su yi rajista, domin INEC a shirye take a kodayaushe.
Ya bayyana cewa da farko akwai rumfunan zabe 4,902 a jihar amma tare da samar da karin rumfunan zabe 6,652 a halin yanzu.