fidelitybank

Abin takaici ɗan Najeriya ba zai iya tafiya cikin ƙwanciyar hankali ba – Ɗantata

Date:

Hamshaƙin ɗan kasuwar nan a jihar Kano, Alhaji Aminu Alhassan Dantata, ya bayyana damuwar sa dangane taɓarɓarewar tsaro da ya dabaibaye Najeriya.

Alhaji Aminu Alhasaan Ɗantata ya bayyana ne hakan ne a bikin ƙaddamar da littafin “Tabswiratul Hukkam” a ɗakin taro na jami’ar Bayero a jiya Asabar.

“Hare-haren ƴan fashin daji da satar mutane domin karbar ƙudin fansa na daga cikin manyan matsalolin da yankin Arewacin Najeriya ke fama da shi”.

Ya kuma ce“Halin da ake ciki yanzu ƴan Najeriya ba su da kwanciyar hankali a kan dukiya da rayuwarsu a lokacin da su ke tafiye-tafiye ko kuma ma a gidajen su”. A cewar Ɗantata.

Alhaji Aminu shi ne ya ɗauki nauyin fassara da buga littafin na Tabswiratul Hukkam, wanda ya ke jawabi a kan shari’ar Muslunci, kuma wannan littafi zai taimakawa alkalai gudanar da jagora a lokacin gudanar da shari’o’i a kotuna.

Mahalarta taron kaddamar da littafin

Taron kaddamar da littafin, ya samu halarcin gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje da Mai Alfarma Sarkin Musulmi Sa’ad Abubakar III da sauran manyan baƙi daga ciki da wajen jihar Kano.

vanguard 
nigeria

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

A na neman kusan Mutane 400 da suka ɓace a ambaliyar Neja

A na ci gaba da ayyukan ceto bayan ambaliyar...

Mun bayar da hutu ranar Litinin bisa jimamin mutuwar ƴan Wasa – Gwamnatin Kano

Gwamnan jihar Kano Abba Kabir Yusuf ya ayyana ranar...

Tun farko na shaida wa Tinubu ba zan zaɓe shi ba – Amaechi

Tsohon ministan sufuri na Najeriya, Rotimi Amaechi ya ce...

Fernandes na duba yiwuwar barin Man Utd zuwa Al-Hilal

Bruno Fernandes na duba yiwuwar ficewa daga Manchester United...

Gwamnatin Tinubu ta jefa al’umma fiye da miliyan 150 cikin tsananin talauci – NLC

A daidai lokacin da gwamnatin shugaban Najeriya Bola Ahmed...

Sojoji sun ce sun hallaka ƴan Ta’adda 60 a jihar Borno

Dakarun sojijin Operation Haɗin-Kai sun ce sun kashe ƴan...

Zan cigaba da jajircewa a kan rantsuwar da na yi ta kujera ta – Fubara

Gwamnan jihar Ribas da aka dakatar, Sim Fubara, ya...

Ambaliya ya kashe Mutane a jihar Neja

Wasu rahotanni sun bayyana cewa, mutane da dama sun...

Kotu ta tabbatar da nasarar Gwamnan Edo

Kotun daukaka kara da ke Abuja ta amince da...

An kashe aƙalla mutum 10,217 a mulkin Tinubu – Amnesty

Wani bincike da ƙungiyar Amnesty International ta fitar kwanan...

Gwamnati ba ta tausayin Talaka – Atiku

Ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar PDP a zaben...
X whatsapp