fidelitybank

Abacha ya yaudari ‘yan siyasa – IBB

Date:

Tsohon shugaban kasar Najeriya, Janar Ibrahim Badamasi Babangida IBB, ya ce, tsohon shugaban mulkin sojin Najeriya, Sani Abacha, wanda ya mulki kasar daga 1993 har lokacin mutuwarsa a 1998, ya hau mulkin ne bayan ya yaudari ‘yan siyasa.

Janar Babangida ya bayyana haka ne a hirarsa da Trust TV yayin da ya ke bayyana yadda Abacha ya yaudari mutane ya kwace mulki.

Abacha, wanda IBB ya bayyana a matsayin “babban abokina”, ya kasance hafsan hafsoshin sojoji a lokacin mulkin Babangida daga 1985, kuma daga baya ya nada shi Ministan Tsaro a 1990.

Babangida ya ce,”Gwamnatin Abacha ta na da wayo. Sun san wadanda suka fi magana a kan zabe da juyin mulkin da batun 12 ga watan Yuni da sauran abubuwa”.

Sai suka fara magana da su, suka yaudare su da karfafa musu gwiwa su kawar da gwamnatin rikon-kwarya, da cewar idan sun kawar da gwamnatin rikon-kwaryar, za su dawo da su, su ba su abin da suke so mulkin dumokuradiyya, daga nan sai a kafa gwamnatin farar hula.

Babangida ya ce: ”Da wannan su ka yaudari jama’a da sauran fitattun mutane, saboda haka da Abacha ya shigo, sai ake ta murna, hankali ya kwanta; Madalla abu ya yi kyau! Abin da zai faru a gaba kuma shi ne zababbiyar gwamnatin dumokuradiyya. Ni na sani, mun sani, hakan ba zai yiwu ba, saboda maganar ita ce: (Abacha zai ce ), Me zai sa in sa kaina cikin hadari, kawai in zo in damka muku mulki?’ Wannan shi ne abin da ya faru.” In ji Babangida.

punch newspaper headlines today

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp