fidelitybank

A yayin da Ronaldo ke kokarin hadewa da Messi shi kuwa Mbappe ya karkata zuwa Liverpool

Date:

Ɗan wasan Faransa Kylian Mbappe mai shekara 23 ya kwadaitu da Liverpool bayan raina kwazon Real Madrid a karawarsu ta zakarun Turai da kungiyarsa ta Paris St-Germain. (Sport, via Star)

A cewar BBC, sai dai, PSG a shirya take ta biya Mbappe makudan kudaden da zai kai shi ga zama ɗan wasa mafi tsada a duniya, za ta ke biyansa kusan £1m a kowanne mako a kokarin hana shi tafiya. (Independent)

Dan wasan Manchester United Cristiano Ronaldo mai shekara 37 na iya haduwa da abokin hamayyarsa ɗan kasar Argentina Lionel Messi mai shekara 34, a kaka mai zuwa a Paris St-Germain(Mirror)

Real Madrid ta soma shirye-shiryen cefano ɗan wasan Arsenal mai shekara 24 Kieran Tierney zuwa Bernabeu. (Calciomercato, via Sun)

Manchester City na ɗab da saye ɗan wasan Brazil Savio mai shekara 17 da ke taka led a Atletico Mineiro(Fabrizio Romano)

Ɗan wasan West Ham da Ingila Declan Rice na fatan burinsa ya cika na komawa Chelsea bayan Thomas Tuchel ya yanke hukuncin dauko Conor Gallagher mai shekara 22. (Standard)

Newcastle na shirin gabatar da tayi kan ɗan wasan Sevilla mai shekara 28 Diego Carlos. (Marca, via Sun)

Arsenal da Manchester City na duba yiwuwar gabatar da tayi kan ɗan wasan Inter Milan mai shekara 24 Lautaro Martinez. (Sun)

Tsohon ɗan wasan Amurka da ya rike koci a Red Bull Salzburg da RB Leipzig Jesse Marsch ya kasance mutum na farko da Leeds United ke fatan ya maye gurbiMarcelo Bielsa mai shekara 66 da shi, mai yiwuwa ya yi bankwana da ita nan gaba kadan. (Telegraph)

Newcastle United ta zuba ido kan ɗan wasan Belgium mai shekara 19 Jeremy Doku, da ke wasa a Rennes kuma ake kiyasta tsadarsa kan £22m. (Chronicle)

Bayan gazawa sau da dama a cinikin ɗan wasan Lille Sven Botman mai shekara 22 a watan Janairu, Newcastle United na shirin gabatar da tayin saye ɗan wasan cikin gaggawa a kaka mai zuwa. (Mirror)

Har yanzu babu wata tattaunawa tsakanin Chelsea da wakilan Antonio Rudiger kan sabon kwantiragin ɗan wasan Jamus mai shekara 28 a Stamford Bridge. (Sky Sports)

Ɗaya daga cikin daraktoci a Sevilla Monchi na da yaƙinin cewa Anthony Martial ba shi da damuwa kuma yana farin ciki bankwana da Manchester United(Metro)

AC Milan ta bi sahun Borussia Dortmund da Barcelona a farautar ɗan wasan Morocco Noussair Mazraoui mai shekara 24, wanda ya sanar da cewa zai bar a Ajax a wannan kakar. (Fabrizio Romano)

Shugaban ƙungiyar Arsenal Vinai Venkatesham ya kare matakansu na kin kashe kudi a kasuwar cinikin ‘yan wasa a watan Janairu. (Sun)

nnn.ng

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp