fidelitybank

A saki Emefiele kafin kwana goma – Kotu

Date:

Wata Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja, ta umarci hukumar tsaron farin kaya ta tuhumi Godwin Emefiele dakataccen Gwamnan Babban Bankin Najeriya a kotu cikin mako ɗaya ko kuma ta sake shi.

Kotun ta ba da wannan umarni ne a lokacin sauraron ƙara da Emefiele ya shigar don tabbatar da ‘yancinsa na ɗan’adam, inda yake ƙalubalantar kamawa da tsare shi da Hukumar DSS take yi.

A ranar Asabar 10 ga watan Yuni ne Hukumar DSS ta ba da sanarwar cewa ta kama tare da tsare, Godwin Emefiele.

Da farko ta ce, Emefiele ba ya hannunta, kafin daga bisani ta tabbatar da cewa ya shiga hannu.

Tun a daren Juma’a ne, wasu rahotanni suka ce jami’an tsaro sun yi awon gaba da shi, jim kaɗan bayan Shugaba Bola Tinubu ya dakatar da shi daga kan muƙaminsa.

“DSS na tabbatar da cewa Emefiele, dakataccen Gwamnan Babban Bankin Najeriya, yanzu haka yana hannunmu don gudanar da bincike,” a cewar wata sanarwa da ta wallafa a shafinta na Twitter.

Shugaban ƙasa Bola Tinubu da jam’iyyarsa ta APC sun zargi Emefiele da yunƙurin hana su cin zaɓen da aka kammala cikin watan Fabrairu saboda tsarin rage kuɗi a hannun jama’a da ya ƙaddamar da kuma canza fasalin naira.

Kafin haka, DSS ta zargi Emefiele da taimaka wa ta’addanci, har ma aka kai shi kotu kan zarge-zargen.

naija legit

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Makami mai Linzami ya faɗa kan cibiyar tattara bayanan sirrin Isra’ila

Kafar yaɗa labarai ta gwamnatin Iran ta ce, ƙasar...

Iran ta ƙaddamar da sabbin hare-haren makamai masu linzami kan Isra’ila

Rundunar sojin Isra'ila ta ce, Iran ta ƙaddamar da...

Isra’ila ta na da makaman nukiliya 90

Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu ya dade yana cewa Iran...

Kashe jagoran Iran Ayatullah shi ne kawo ƙarshen rikici – Isra’ila

Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu ya ce duk wani shiri...

Jerin sunayen masu Fashin Waya 51 da aka kama a Kano

Rundunar ƴansandan Kano, ta fitar da jerin sunayen Mutane...

Iran ta dakatar da tashin jirgi a ƙasarta

Hukumar kula da zirga-zirgar jiragen sama ta Iran ta...

Poland za ta kwashe dukkannin ƴan ƙasarta daga Isra’ila

Poland na shirin kwashe kusan ‘yan kasarta 200 daga...

Kisan Binuwai abun haushi ne bai kamata a ƙyale ba – Atiku

Atiku Abubakar ya yi Allah-wadai da Kisan Benue, tare...

Ƴan Bindiga sun ajiye makamai a Katsina

Wasu fitattun jagororin ƴanbindiga da suka addabi yankunan ƙaramar...

Iran ta rataye Mutumin da ya yi mata leƙen asiri

Iran ta ce ta aiwatar da hukuncin kisa ga...

Isra’ila ta ci gaba da neman Mutanen da suka maƙale

Tawagar masu aikin ceto a Isra'ila na ci gaba...

Kotu ta bayar da umarni a kashe Matashi ɗan shekara 23 a Kano

Babbar kotun jihar Kano mai lamba 23 ƙarƙashin mai...
X whatsapp