fidelitybank

A karo na farko mata sun gudanar da gasar tseren Doki a Saudiyya

Date:

Matan kasar Saudiyya sun zama zakara a gasar tseren doki da a ka gudanar na Sarki Abdulazizi.

Matan mahaya dawakai 10 ne suka yi nasara cikin 38 da suka fafata a gasar tsere karo na shida yayin bikin Raƙuma na Sarki Abdulaziz wanda ya gudana a ranar Asabar.

Jaridar Saudi Gazette ta rawaito cewa, wannan shi ne karo na farko da matan su ka fara tseren dokin a kasar Saudiyya.

Daruruwan ‘yan kallo sun taru domin kashe Kwarkwatar idanun su yayin gudanar da tseren da mata suka fafata a karon farko a tarihin bikin.

Wannan ne karon farko da aka ƙaddamar da zagayen ‘yan ɗai-ɗai a tseren wanda a ke gudanarwa a filin da ya kai faɗin murabba’in kilomita 32 a yankin Sayahadah.

Waɗanda su ka yi nasara a tseren za su samu kyautar kuɗi riyal miliyan 88, mafi girma a duniya a tsren dabbobi.

An shigar da mata gasar ne da zimmar ƙarfafa musu gwiwar shiga al’amura sanye da tufafinsu na gargajiya da kuma faɗaɗa azuzwan masu shiga gasar.

 

latest legit news

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp