fidelitybank

A gaggauta gudanar da binciken turmutsutsun da aka yi a wasan Kamaru – Paul Biya

Date:

Shugaban kasar Kamaru Paul Biya, ya bayar da umarnin gudanar da bincike kan abin da ya janyo aka yi turmutsutsun da ya yi sanadiyyar mutuwar mutum takwas a wajen filin wasa a babban birnin kasar Yaoundé kafin wani wasana gasar cin kofin Afirka.

Wata sanarwa da gwamnati ta fitar ta ce, binciken zai sa a gano abin da ya haddasa lamarin.

Turmutsutsun ya faru ne a lokacin da magoya baya suka yi kokarin kutsawa cikin filin wasan Olembe kafin karawar Kamaru da Komoros (Comoros) .

Bayan wadanda suka rasa ransu, wasu mutum talatin kuma sun ji rauni.

Ba a dai tsara cewa, mutane da yawa za su shiga kallon wasan ba, saboda matakan kariya na cutar korona, amma wadanda suka ga abin da ya faru sun ce tarin magoya baya sun je domin shiga cikin filin.

Hukumar kwallon kafa ta Afirka (Caf), wadda ta shirya gasar ita ma ta kaddamar da nata binciken.

Kamaru wadda ta yi nasarar zuwa wasan dab da na kusa da karshe bayan ta doke Komoros da ci 2-1, a wasan, yanzu za ta kara da Gambia, wadda ita kuma ta ci Guinea 1-0.

latest news in nigeria today 
2021 ripples

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp