fidelitybank

A dawo da tallafin aikin Hajji ga maniyyatan Najeriya – Ndume

Date:

Jagoran ƴan kwamitin majalisar dattijawa kan harkokin ƙasashen waje a lokacin aikin hajjin 2025, Sanata Ali Ndume ya buƙaci da a mayar da tsarin bayar da tallafi kan batun aikin hajji a ƙasar domin rage tsadar kujera ga maniyyata.

Ndume ya fadi haka ne a tattaunawarsa da BBC jim kadan bayan kammala aikin hajjin 2025 a ƙasar Saudiyya.

Sanatan wanda ya nuna gamsuwa kan tsarin da aka samar ga mahajjatan Najeriya a Saudiyya ya ce “dama gwamnatin da ta shuɗe ita ce ta cire tallafin da ake bayarwa kan aikin hajji, saboda haka ya kamata a dawo da bayar da tallafi saboda aikin hajjin ya yi tsada.”

Mahajjatan Najeriya a 2025 sun biya kuɗin kujera ne tsakanin naira miliyan 8.3 zuwa miliyan 8.8 dangane da ɓangaren ƙasar da suke zama.

Hakan ya ɗara abin da maniyyatan Najeriya suka biya kan kujerar aikin hajji a bara – 2024, inda suka biya fiye da naira miliyan shida a kan kujera.

Sai dai batun aikin hajji a Najeriya a shekarar 2024 ya kasance mai cike da ruɗani sanadiyyar zargin badaƙala da rashin kyakkyawan tsari, lamarin da ya kai ga bincike da kuma sauke shugaban hukumar.

Farashin kujerar aikin hajji ya ci gaba da tashi a Najeriya shekara bayan shekara, lamarin da yawanci akan ɗora alhakin kan zubewar darajar takardar kudin ƙasar – Naira.

nigeria.news

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp