Shugaban Amurka Joe Biden, ya ce, lokaci ya yi da ya kamata a kawo ƙarshen tambayoyin da ake yi game da takararsa a zaɓen shugabancin ƙasar
A takardar da ya aike wa ƴan jam’iyyar Dimocrat a majalisar dokokin ƙasar, Mista Biden ya ce jam’iyyarsa tana da aiki guda a gabanta – kayar da Donald Trump.
Ya ce rashin fayyace batun ba abin da yake sai taimaka wa ɗantakarar na jam’iyyar Republican.
Ana samun ƙaruwar ƴanmajalisar jam’iyyar Dimocrat da ke nuna shakku kan ko Biden mai shekara 81 a duniya zai iya lashe zaɓe tun daga muhawarar da suka tafka da Trump


