fidelitybank

A ci gaba da tsare matar Abdulmalik a gidan gyaran hali – Kotu

Date:

Kotu ta umarci ‘yan sanda su ci gaba da tsare Jamila Muhammad, matar mutumin da ake zargi da kisan Hanifa Abubakar mai shekara 5 a Jihar Kano.

A na zargin Jamila mai shekara 30 da haɗa baki wajen ɓoye yarinyar da mijinta Abdulmalik Tanko ya sato, da ƙulla makirci, da sace mutum, da kuma kisan kai.

Da yake karanto tuhumar da ake yi mata, lauya mai shigar da ƙara ya ce ana zargin ta da ɓoye wadda aka yi garkuwa da ita tsawon kwana biyar.

Jamila ta ƙaryata rahoton farko da aka bayar wanda ya zarge ta da ɓoye Hanifa a gidanta.

Idan ba a manta ba, Abdulmalik ya faɗa wa ‘yan sanda cewa bayan ya sace Hanifa ya kai ta wajen matarsa ne, inda ta zauna a gidan kafin daga baya ya kashe kuma ya binne ta a farfajiyar makarantarsa da ke Kwanar Dakata ta Ƙaramar Hukumar Nasarawa a birnin Kano.

Kotun Majistaren da ke Gidan Murtala ta ɗage zaman zuwa 2 ga watan Fabarairu tare da uamrtar ‘yan sanda su ci gaba da tsare Jamila.

Gwamnan Kano Abdullahi Ganduje ya ce, a shirye yake ya sanya hannu kan zartar da hukunci idan kotu ta yanke wa Abdulmalik hukuncin kisa.

labaran duniya na yau

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Dino Melaye ya gudu daga PDP ya faɗa ADC

Tsohon ɗan jamalisar dattawa mai wakiltar Kogi ta Yamma,...

Isra’ila na zargin Canada da goyon bayan Hamas – Netanyahu

Isra'ila ta zargi Canada da taimaka wa Hamas bayan...

Rashin tallafin agaji ka iya dawo da Boko Haram a Najeriya – MDD

Hukumar Samar da Abinci ta Majalisar Dinkin Duniya ta...

Yin gini a kan hanyoyin ruwa ne ya janyo ambaliyar Maiduguri – NEMA

Hukumar bayar da agajin gaggawa da Najeriya NEMA ta...

Amnesty ta yi Allah wadai da tsare Sultan kan bidiyon lafiyar Tinubu

Ƙungiyar kare haƙƙin bil'adama ta Amnesty International ta yi...

Dalilin da ya sa na gana da Tinubu – Kofa

Ɗan majalisar tarayyar mai wakilitar Kiru da Bebeji daga...

Ba za mu jingine yajin aiki ba har sai an biya mana buƙatun mu – Ma’aikatan Jinya

Shugaban ƙungiyar ma'aikatan jinya ta Najeriya, Morakinyo-Olajide Rilwan ya...

Za a fara yi wa Dalibai gwajin kwaya kafin su shiga jami’a – NDLEA

Gwamnatin Tarayya ta ce, za ta fara yi wa...

Za mu kammala titin jirgi na Kaduna zuwa Kano a 2026 – Gwamnati

Gwamnatin Tarayya, ta ce za a kammala aikin titin...

Adadin kudaden da Liverpool ta kashe wajen daukar ‘yan wasa

Liverpool ta kashe fam miliyan 265 wajen ɗauko ƴanƙwallon...

Sunderland ta ɗauko ƴanƙwallo bakwai a kakar bana

Granit Xhaka ya zaman ɗan ƙwallo na bakwai da...

James Trafford ya sake komawa Man City daga Burnley

Mai tsaron ragar tawagar Ingila, mai shekara 21, James...
X whatsapp