Kotu a jihar Legas ta daure wani mahaifi mai shekaru 42, zai sha ɗaurin rai-da-rai ba tare da zaɓin biyan tara ba, bayan kotun hukunta laifukan cin zarafi ta same shi da laifin yi wa ‘yarsa mai shekara 15 fyaɗe da kuma yi mata ciki.
Kotun da ke Jihar Legas ta kama Ekpo Lawrence da laifin ne a jiya Alhamis, bayan da mai shari’a, Abiola Soladoye ta ce, kotun ta yi nasarar tabbatar da zargin da gwamnatin Legas ta gabatar kan mista Lawrence.
Kamfanin dillancin labarai na NAN ya rawaito cewa, mai shari’ar ta ce, hujjojin da masu shigar da ƙarar suka bayar sun yi daidai, yayin da shi kuma wanda ake zargi ya yi ta sauya zance.
Ta ƙara da cewa, musanta zargin da mutumin ya yi da gangan ne, domin ya karkatar da hankalin kotu. Ta ce, “Abain kunyar da wanda ake zargin ya aikata ya ƙazanta, kuma ba abin yafewa ba ne a ƙarƙashin sashe na 137 na Dokokin Manyan Laifuka na Jihar Legas na shekarar 2015, sannan abin Allah-wadai ne ta kowace fuska,” in ji Mai Shari’a Soladoye.
kamfanin dillancin labarai na Kasa NAN ta rawaito cewa, masu shigar da ƙara sun ce mutumin ya aikata laifin ne tsakanin watan Disambar shekarar 2018 zuwa watan Yunin 2019.