Gwamnan jihar Rivers, Nyesom Wike, a ranar Talata ya rusa majalisar zartarwa ta jihar.
Shugaban ma’aikatan gwamna Emeka Woke da kuma babban mataimaki na musamman, Harold Koko, suma an sauke su daga mukamansu.
Gwamnan ya umurci daukacin tsoffin ‘yan majalisar zartarwa na Jiha da su mika su ga manyan jami’ai a ma’aikatun su.
“Mai girma Gwamna Nyesom Wike, ya yabawa ‘yan majalisar zartarwa na jihar Ribas, bisa hidima da gudunmawar da suke bayarwa wajen ci gaban jihar. Ya kuma yi musu fatan alheri a dukkan ayyukansu na gaba,” in ji mataimaki na musamman ga gwamnan kan harkokin yada labarai, Kelvin Ebiri a cikin wata sanarwa.
Kawo yanzu dai ba a san dalilin da ya sa gwamnan ya dauki matakin ba zato ba tsammani ba, amma majiya daga fadar gwamnatin ta ce, yana shirin cusa sabbin ƴan majalisar zartaawa a cikin tsarin gabanin zaben 2023 da kuma ba da dama ga wasu mambobin zartaswa da ke shirin tsayawa takarar kujerar gwamna da kuma ba da dama.