Gamayyar kungiyoyin ma’aikatan da ke aiki a bangaren sufurin jirgin sama a Najeriya sun janye yajin aikin da suka shirya yi.
Kungiyoyin sun fasa daukar matakin ne bayan da suka rattaba hannu kan wata sabuwar yarjejeniya da gwamnatin Najeriya yayin wani zama na musamman da aka yi a shalkwatar ma’aikatar kwadago ta Najeriya a ranar Litinin a Abuja.
A cewar BBC, manyan batutuwan da suka janyo barazanar yajin aikin sun hada da rashin biyan ma’aikata sabon albashi mafi kankanta, wanda tun 2019 ya kamata a fara biya.
Batu na biyu kuma shi ne jinkirin fara amfani da sharuddan aiki kamar yadda suka shafi ma’aikatan da ke aiki a hukumomin gwamnatin tarayyar Najeriya.
Ministan kwadago da ayyukan yi, Chris Ngige ya tabbatar da kulla yarjejeniyar:
“Mun yarda tsakaninmu cewa hukumar da ke tsara albashin ma’aikata a Najeriya za ta aika wa dukkan ma’aikatu da hukumomin gwamnatin tarayya – har da wadanda ba ma’aikatan gwamnati ne ba – wata wasika da ke fayyace matakan da ya dace su dauka kan biyan albashin ma’aikata karkashin dokar Albashi ta bai daya na 2019.”


