fidelitybank

Hisba ta kama kwalaben giya 1,906 a Jigawa

Date:

Hukumar Hisbah ta jihar Jigawa ta kwace kwalaben giya 1,906 a wani sumamen da ta kai a lokuta daban-daban a fadin jihar a shekarar da ta gabata, 2021.

Kwamandan rundunar, Mallam Ibrahim Dahiru ne ya shaidawa kamfanin dillancin labaran kasa NAN, a Dutse, babban birnin jihar, a ranar Talata, 25 ga watan Janairun 2022.

Mallam Ibrahim ya ce, sun yi nasarar kwace giyar ne a otal-otal da wuraren shan barasa daban-daban a fadin jihar.

Shugaban Hisbar ya kuma ce, “Mun kama mutum 92 da muke zargi da aikata laifuka na badala daban-daban, wadanda suka hada da karuwai a lokacin sumame. Laifukan da ake zargin mutanen sun aikata sun hada da caca da yawan-ta-zubar da shirya liyafar casu a lokacin biki da sauransu”, in ji kwamandan.

Haka kuma ya ce a tsawon lokacin Hisbah ta rufe gidajen karuwai.

Mallam Ibrahim ya kara da cewa, an mika kwalaben giyar da aka kwace da mutanen da aka kama ga ‘yan sanda, domin kara bincike.

legit latest news

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp