Masu gabatar da kara a Masar suna binciken wani mutum da ake zargin ya rubuta wa daya daga cikin ‘yan wasan kasar da ke gasar cin kofin kwallon kafa na Afirka a Kamaru, Mostafa Mohamed, jarrabawa.
Kafafen yada labarai na kasar sun ruwaito cewa an ankarar da jami’an tsaro kan zargin magudin jarrabawa a wata makaranta mai zaman kanta a birnin Giza.
Kafofin sun ce, ana tsare da wani mutum , wanda ya ce shi abokin Mostafa ne kuma wai yana son ya taimake shi ne.
Zuwa yanzu dai babu wasu bayanai da aka ji daga dan wasan kwallon na Masar, kan wannan lamari na zargin rubuta masa jarrabawa. A cewar BBC.