fidelitybank

Mutane 8 sun mutu yayin shiga filin wasa a Kamaru

Date:

Rahotanni na nuni da cewa, akalla mutune takwas ake zargin sun mutu yayin da 38 suka jikkata, sakamakon wani turmutsitsi da ya auku a wajen filin da ake buga gasar cin kofin nahiyar Afirka ta Afcon a Kamaru.

Hotunan bidiyo sun nuna yadda ‘yan kallo suka rinÆ™a kokowar shiga fili wasa na Paul Biya da ke birnin Yaounde.

Naseri Paul Biya, wanda shi ne gwamnan yankin tsakiyar Kamaru, ya ce akwai yiwuwar a samu karin mutanen da abin ya shafa, a cewar kamfanin labarai na AP.

Wani rahoton kuma na cewa akwai yara da dama da suka suma.

Filin wasan na iya daukar mutum dubu 60, amma saboda matakan da ake É—auka saboda annobar korona ba a yarda a haura kashi 80 cikin 100 na wannan adadin ba.

Jami’ai sun ce mutum dubu 50 ne suka yi kokarin shiga filin wasan domin kallo.

Malaman jinya Olinga Prudence ta shaidawa kamfanin dillancin labarai na AP cewa, wasu daga cikin mutanen da suka jikkata na cikin yanayi na galabaita.

Hukumar kwallon kasashen Afirka, CAF a wata sanarwa ta ce tana bincike kan lamarin domin samun ƙarin bayanai kan ainihin abin da ya faru.

An dai fafata a zagaye na biyu na gasar tsakanin Cameroon da Comoros duk da faruwar wannan al’amari, kuma mai karban bakwancin wasan ta yi nasara da 2-1.

legit ng

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp