Dan majalisar wakilai mai wakiltar mazabar Tarauni a jihar Kano, Hafizu Kawu, ya bayyana mataimakin shugaban kasa, Yemi Osibanjo, a matsayin wanda zai gaji shugaban kasa Muhammadu Buhari a zaben 2023.
Da yake jawabi ga manema labarai a Kano ranar Litinin, Kawu, wanda tsohon mai taimaka wa Osibanjo ne, ya ce mataimakin shugaban kasar na da abin da a ke bukata, domin ya gaji Buhari saboda “kwarewa da kwazonsa wajen tafiyar da ayyuka”.
Dan majalisar ya ce, duk da cewa har yanzu mataimakin shugaban kasar bai bayyana aniyarsa ta tsayawa takarar shugaban kasa ba, shi ne ya fi dacewa ya gaji Buhari.
A cewarsa, Osibanjo ya na dagogewa, da kuma iya shugabancin Najeriya a kan duk wani mai neman tsayawa jam’iyyar APC.
Ya ce: “Mataimakin shugaban kasar na da karfin inganta tattalin arzikin kasar ganin cewa shi ne ya tsara duk wani shiri na zuba jari da ya shafi miliyoyin ‘yan Najeriya.
“Na tabbata mataimakin shugaban kasa zai ci gaba daga inda shugaban ya tsaya, domin ya na da tunanin bunkasa Najeriya. Shi ne magajin shugaban kasa. Nijeriya ta na cikin zuciyarsa. Na yi imani sosai a Najeriya. Shi shugaba ne na misali.
“Shi mataimaki ne mai aminci kuma aikinsa a matsayin Mataimakin Shugaban kasa ba a taba ganin irinsa ba. Ko da ya zama shugaban kasa a lokuta da dama, Osibanjo ya taka rawar gani sosai, domin haka ya na da kwarewar zama shugaban kasa a 2023, “inji Kawu.