fidelitybank

2022: Siyasar zage-zage za ta iya kawo cikas a Najeriya – Orji Kalu

Date:

Tsohon gwamnan jihar Abia kuma bulaliyar majalisar dattawa, Dr. Orji Kalu ya bukaci ‘yan Najeriya da su jajirce tare da kishin kasa da kuma nuna kyakkyawan fata, domin shiga sabuwar shekara a sa’a.

Kalu yayin da ya ke jinjina wa ‘yan kasar kan yadda su ke ci gaba da marawa shugaban kasa Muhammadu Buhari baya, ya gargadi ‘yan siyasa da su guji yin siyasar zage-zage da za su iya kawo cikas ga kasar nan.

Tsohon Gwamnan ya jaddada cewa, dole ne shugabanni a kowane mataki na gwamnati su tabbatar da jin dadin al’umma, shi ne babban abin da zai sa a gaba a manufar su, ya kuma kara da cewa, dole ne gwamnati da masu mulki su taka rawar da za ta dace wajen gina kasa ta Najeriya mai ci gaba, hadin kai da mai dorewa.

Kalu, wanda ya bayyana haka a gidansa na Igbere, a lokacin rabon kyaututtukan karshen shekara ga al’ummar mazabarsa a wani bangare na ayyukansa na karshen shekara, ya yi kira ga ‘yan Najeriya masu kishin kasa da su rungumi ayyukan jin kai.

Ya ce, “Sabuwar shekara, ya zama wajibi mu yi la’akari da nasarorin da mu ka samu da kalubalen da mu ka samu a daidai ku da kasa baki daya”.

“Babu shakka, 2021 shekara ce ta tunani da kuma biki.

“Domin kasar nan ta kai wani matsayi na kishi, dole ne mu guji ayyukan da za su raba kasar nan.

“Lokaci ya yi da ‘yan Nijeriya ba tare da la’akari da bambance-bambancen siyasa, kabilanci da addini ba, ya kamata su wanzar da zaman lafiya da juna a wani yunkuri na gina al’umma mai adalci.

“Ba wata kasa da za ta ci gaba a cikin yanayin rashin jituwa.

“Dole ne a yi amfani da bambancin al’adu da kabilanci da addini a Najeriya domin ci gaban kasar.

“Bai kamata mu bar ra’ayin siyasa ko addini ya mayar da Najeriya baya ba.

“Bari mu sanya mutane cikin gwamnati cikin zarge-zarge masu ma’ana da suka saba wa kalaman kyama da yakin neman zabe.

“A cikin sabuwar shekara, dole ne mu yi kyawawan halaye a cikin ayyukan mu na yau da kullun, domin tabbatar da zaman lafiya da hadin kai.” Inji Kalu.

Tsohon Gwamnan ya yi wa ‘yan Najeriya fatan nasara a sabuwar shekara.

nigeria daily post

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp