Shugaba Muhammadu Buhari ya ce gwamnatinsa ba za ta naɗe kafa ta na kallo ƴan bindiga su ci gaba da cin Karen su ba babbaka ba a sabuwar shekarar 2022.
Buhari ya ce da yawan ƴan bindigar na miƙa wuya ga dakaru a halin da a ke ciki, kuma an samar da tsare-tsare da za su ba su damar ci gaba da yin hakan a wurare daban-daban’.
BBC ta rawaito cewa, a sakonsa na barka da arziƙin shiga sabuwar shekara, shugaban ya ce gwamnatinsa za ta bayar da himma ga bangaren fasahar zamani, domin sama wa matasan ƙasar abun yi, da kuma bunkasa tattalin arziƙi.
Ya ce, “Rashin tsaron da ake fama da shi a wasu sassan kasar nan na iya yin barazana har jama’a su kasa ganin irin nasarorin da aka samu a zahiri a fannin tattalin arziki da kuma manufar gwamnati ta sanya al’ummar kasar nan a kan turbar da ta kamata, amma ina son in tabbatar muku cewa za mu ci gaba da tsayawa tsayin daka a kan alkawuranmu kuma za mu ci gaba da aiwatar da shirye-shiryenmu da tsare-tsarenmu,” inji shi.