fidelitybank

Ƴan ta’adda sun ƙona fasinjoji 42 a cikin mota a Sokoto inda 37 su ka rasu nan take

Date:

 

Rahotanni daga Jihar Sokoto sun baiyana cewa ƴan ta’adda sun ƙona wata motar fasinja ɗauke da mutum 42.

Rahotanni sun baiyana cewa mutum 37 sun ƙone ƙurmus, inda biyar kuma su ka tsira da raunuka daban-daban.

BBC Hausa ta rawaito cewa fasinjojin sun fito ne daga Ƙaramar Hukumar Sabon Birni da ke jihar domin yin ƙaura zuwa wasu yankunan Najeriya, saboda ta’azzarar ayyukan ƴan bindiga a inda suke.

Wasu shaidu sun cewa BBC Hausa cewa lamarin ya faru ne da misalin karfe 9 na safiyar ranar Litinin.

“Motar ɗauke da fasinjojin ta tashi daga Sabon Birni, ta yi tafiyar da bai fi kilomita shida ba zuwa kauyen Gidan Bawa inda wannan masifa ta afka mata,” kamar yadda waɗanda suka yi aikin ceton suka bayyana wa BBC.

Tuni dai aka yi jana’ziar mamatan in ji shaidu.

Wani ganau ya cewa BBC: “Lokacin da abin ya faru ina Sabon Birni aka kira ni aka shaida min. Daga cikin matafiyan ma har da wani ƙanin mahaifiyata da matarsa da ƴaƴansu huɗu.

“Cikin ƴaƴan Allah Ya yi wa biyu rasuwa. Lokacin da muka isa wajen da ya faru mun je mun iske mutane sun mutu, kuma a ƙalla mun ƙirga gawarwaki sun kai 25,” ya ce.

Ya ƙara da cewa akwai tsirarun mutane daga cikinsu da suka tsira.

Shi ma wani shaidan da ya buƙaci a sakaya sunansa ya ce “mutum 45 ne a cikin motar, amma bakwai ne suka tsira da rayukansu, su ma a yanzu haka suna cikin halin ha’ula’i.

“Babu maganar ma ka ga gawa a kammale, sai dai muka dinga haɗa ƙafafu da hannaye daban-daban aka yi musu jana’iza a tare.”

Ya ce shi yana tsaye a tasha ma lokacin da motar ta tashi. “Ƴan Union ne ma na tasha suka gaya mana adadin mutanen da motar ta tashi da su,” a cewarsa.

Yankin arewa maso yammacin Najeriya na ɗaya daga cikin yankunan da suka fi fama da matsalar tsaro a Najeriya, sai dai a lokuta da dama gwamnatocin yankin na cewa suna iya kokarinsu domin tabbatar da kare rayuka da dukiyoyin al’umarsu, abin da al’umar ke cewa ba sa gani a kasa.

kano news

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp