fidelitybank

Covid-19: Da yiwuwar adadin talakawa su karu a shekarar 2022

Date:

Gwamnatin Tarayya ta ce akwai yiwuwar yawan talakawa su karu zuwa miliyan 109 nan da karshen shekarar 2022.

Ministar Kudi, Kasafi da tsare-tsare, Zainab Ahmed ce ta bayyana hakan, ta ce sabbin mutum miliyan 11 na iya fada wa kangin talauci a cikin shekarar, sakamakon annobar COVID-19.

Zainab Ahmed ta furta hakan ne a Abuja ranar Talata, a ci gaba da taron da ake yi kan annobar COVID-19 mai taken ‘Fadan karshe wajen yaki, tare da murmurewa daga annobar COVID-19’.

Ministar, wacce ta sami wakilcin Darakta Janar na Ofishin Kasafin Kudi, Ben Akabueze, ta ce”Akalla mutum miliyan biyu ne suka fada talauci a 2020, saboda yadda yawan jama’a ya zarce karfin tattalin arzikin kasa, annobar ta COVID-19 da kuma karyewar tattalin arziki sun kara yawan wasu matalautan da kimanin miliyan 6.6, lamarin da ya kawo adadin zuwa miliyan 8.6 a cikin shekarar kawai. Hakan na nuni da yiwuwar karuwar talakawa a Najeriya daga miliyan 90 a 2020 zuwa miliyan 109 a 2022”. A cewar Zainab.

Jaridar Aminiya ta alakanta kalubalen da yawan karuwar ayyukan da ba su da tabbas, wadanda ta ce su ma sun dada jefa jama’a cikin kangin talaucin.

vangurd 
news

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Tinubu ya miƙa saƙon ta’aziyya ga mutanen Kano da Kaduna da Borno

Shugaba Bola Tinubu ya yi Alla-wadai da kisan wasu...

Amurka ta tafka babban kuskure – Iran

Ministan harkokin wajen Iran, Abbas Araghchi ya yi Alla-wadai...

Trump ya yaudari Amurkawa da Iran – Aragachi

Ministan harkokin wajen Iran, Abbas Araghchi ya bayyana cewa...

Sai an hukunta Mutanen da suka kashe ƴan ɗaurin aure – Uba Sani

Gwamnan jihar Kaduna Uba Sani ya yi Alla-wadai da...

An fara binciken fashewar wani abu da ya kashe mutane 5 da jikkata da dama a Kano

Wani abin fashewa da ake tunanin bom ne ya...

An samu fashewar wani abu a kamfanin ƴan Chana a Kano

An samu fashewar wani abu a Kamfanin Ƙarfe na...

Ma’aikacin kamfani ya kashe abokin aikinsa a Kano

Rahoton da ke yawo a kafafen sada zumunta ya...

Kotu ta ɗaure Matashin da yake tare titi a Kano da sunan barƙwanci

Kotun majistire da ke unguwar Nomansland a Kano, karkashin...

Bayan kashe Soja yanzu haka an kama ƴan Daba 398 a Kaduna

Rundunar 'Yan Sandan Jihar Kaduna, ta sanar da kama...

Shettima zai san makomarsa bayan taron APC na ƙasa – Fadar Shugaban Ƙasa

Fadar shugaban ƙasa ta bayyana cewa, sai bayan babban...

Kotu ta ɗaure Matashin da ya shiga ɗakin kwanan Ɗalibai Mata a Kano

Babbar Kotun Shariʼar Musulunci da ke Kofar Kudu a...

Ban gudu daga PDP ba – Namadi Sambo

Tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Mohammed Namadi Sambo, ya ƙaryata...
X whatsapp