fidelitybank

Ƴan Sanda sun cafke tsohon Kwamishinan Ganduje kuma ɗan adawar sa

Date:

‘Yan Sanda sun kama Muaz Magaji, ɗaya daga cikin masu sukar gwamnan Jihar Kano Abdullahi Ganduje.
Ƴan sanda sun kama shi ne bayan wata hira da aka yi da shi kai tsaye a gidan talabijin na Trust TV da ke Utako, Abuja da misalin karfe 9:15 na dare.
Ko da yake har yanzu ƴan sanda ba su ce uffan ba kan kamun nasa, shaidun gani da ido  sun shaida wa jaridar DAILY NIGERIAN cewa jami’an ƴan sanda sun biyo Magaji a baya bayan ya bar ofishin gidan talabijin ɗin.
“Bayan ‘yan mintoci da suka gabata wani abin takaici, damuwa da nadama ya faru a hanyar Ngozi Okonjo Iwela ta hanyar TOS Benson Crescent junction. Injiniya Magaji Muazu ya yi hatsari ne inda a ka hankaɗa motarsa ​​kirar Honda ta sauka daga kan titin sannan ta daki wata sandar fitilar titi. Duk da cewa ya fito daga cikin motar bai ji rauni ba, amma duk jakunkunan Airbags sun fito waje.
“Da alama aikin ‘yan sanda ne domin nan take su ka kama shi su ka kai shi caji-ofis na Utako da ƙarfin tsiya. Yayin da nake rubuta wannan bayani na kasance a wurin ina tsare motarsa ​​kuma yanzu muna kan hanyarmu ta zuwa ofishin ‘yan sanda. Jakarsa da batirin motarsa ​​suna tare da ni,” inji wani ganau.
A tuna cewa a ranar 17 ga watan Janairu, ‘yan sanda a Kano sun gayyaci Magaji domin ya amsa tambayoyi dangane da karar da aka shigar a kan sa.
Sai ya aika lauyoyinsa zuwa ga rundunar maimakon ya bayyana a gabansu da kan sa, sannan ya shigar da kara na tabbatar da tsaro a kan ‘yan sanda.
Ganduje ya kori Magaji, wanda tsohon kwamishinan ayyuka da aiyukan more rayuqa saboda “kalaman rashin ɗa’a” da ya yi kan rasuwar shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa, Abba Kyari.
Tun bayan barin gwamnati, tsohon kwamishinan ya rika sukar gwamnan kan salon shugabancinsa da kuma shigar da iyalansa cikin harkokin mulki a jihar.
Biyo bayan fitowar bangaren jam’iyyar APC a jihar na Sanata Shekarau, sai tsohon kwamishinan ya koma bangaren.

news today in nigeria 2022

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Najeriya na neman dala biliyan 25 na bututun iskar gas zuwa Turai

Najeriya na neman dala biliyan 25 a matsayin kuɗin...

‘Yan sa-kai biyu ne suka mutu a harin da muka kai Zamfara – Sojoji

Rundunar sojin sama ta Najeirya ta tabbatar da kai...

Dakarun sojin ruwa a Najeriya sun yi kaɗan wajen tsaron ƙasa – Emmanuel Ogalla

Babban hafsan sojin ruwa na Najeriya ya ce dakarunsa...

Juma’a da Litinin ranakun hutun Sallar Layya – Gwamnati

Gwamnatin Tarayya ta ayyana ranakun Juma'a da Liitnin masu...

Gwamnatin Neja zai haɗa kai da matatar Ɗangote wajen haƙo ɗanyen man fetur

Gwamnan jihar Neja, Umar Bago, ya nemi aikin haɗin...

Tchiani ya zargi Najeriya, Faransa, China da Amurka wajen cutar da Nijar

Shugaban sojin Nijar, Janar Abdourahmane Tchiani, ya zargi Najeriya...

An ceto yara 12 da aka yi safararsu a jihar Abia

Rundunar ‘Yan Sandan Najeriya ta ce jami'anta sun samu...

A na neman kusan Mutane 400 da suka ɓace a ambaliyar Neja

A na ci gaba da ayyukan ceto bayan ambaliyar...

Mun bayar da hutu ranar Litinin bisa jimamin mutuwar ƴan Wasa – Gwamnatin Kano

Gwamnan jihar Kano Abba Kabir Yusuf ya ayyana ranar...

Tun farko na shaida wa Tinubu ba zan zaɓe shi ba – Amaechi

Tsohon ministan sufuri na Najeriya, Rotimi Amaechi ya ce...

Fernandes na duba yiwuwar barin Man Utd zuwa Al-Hilal

Bruno Fernandes na duba yiwuwar ficewa daga Manchester United...
X whatsapp