Kotun shari’ar musulunci a Kano ta yankewa wata mata hukuncin ta share unguwar su da tsintsiya, sakamakon samun ta da laifin kalmar Karuwa da ta fadawa makociyar ta.
Matar mai suna Rabi ta fara aiwatar da hukuncin da alƙalin kotun Shari’ar Musulunci ta ya yanke mata, sakamakon kama ta da laifin yi wa maƙociyarta ƙazafin “Karuwanci”.
Mai shari’a Halhalatul Khuza’i ne ya kama Rabi mazauniyar Rijiyar Zaki da laifin, sannan ya yanke mata hukuncin share titin unguwarsu baki ɗaya na tsawon kwana 30.
Malama Rabi ta ce ba ta da wani ƙorafi game da hukuncin da aka yanke mata, ta na mai cewa ta ji daɗi da hukuncin bai wuce hakan ba dama tunda baki shi ke yanka wuya.