Rahotanni daga jiha Kwara, na nuni da cewa, wasu da a ke zargin ƴan bindiga ne sun sace mutum biyar ciki har da tsohon jami’in hukumar Kwastan a hare-hare daban-daban da suka kai a ƙananan hukumomi biyu a jihar.
Gidan talabijin na Channels ne ya tabbatar da hakan cewa, harin na farko ya faru ne a Egbejila da ke kan hanyar ƙauyen Obate duk a Ƙaramar Hukumar Asa.
A yayin harin, an sace wani tsohon mataimakin kwanturola na kwastam mai suna, Mohammed Zarma, wanda aka sace shi a gonarsa yayin da ya ke kiwon kifi.
Rahotanni sun bayyana cewa ƴan bindigan sun kutsa gonar ne da bindigogi ƙirar AK-47, inda suka yi awon gaba da shi cikin daji.
Ɗayan harin ya faru ne a kan hanyar Obo Aiyegunle zuwa Osi da ke Jihar Ekiti inda ƴan bindigan suka sace wani bakanike da matarsa mai juna biyu da wasu mutum biyu da ke koyon sana’ar kanikanci.