fidelitybank

Ƙungiyar Adaidaita Sahu sun kai ziyarar godiya ga Baristan da ya tsaya musu

Date:

Dandazon matuka baburan adai daita sahu a jihar Kano sun kaiwa lauyan nan mai zaman kansa ziyarar godiya tare da sake jin sakamako kan lamarin har gida.

Lauyan mai suna Abba Hikima Fagge, wanda shine ya tsaya musu har aka sami sulhu tsakanin gwamnatin da matuka baburan a jihar a matsayin sa na lauyan su.

Da ya ke zantawa da Alkiblah, bayan sun kammala da yammacin ranar Asabar, Barista Abba Hikima Fagge, ya ce, “Mun je ne domin mu kara jin matsayar da aka cimma da gwamnati, sannan mu yi godiya da abun da ya yi musu”.

Dandazon ƴan ƙungiyar

“Mun hadu da su ne a wani filin dake kan titin Airport, kuma na kara basu wasu shawarwari”

“Bayan mun gama sun biyo ni har gida inda suka gaishe da mahaifiya ta tare da yi mata addu’a” In ji Abba.

Inda suka sako shi a gaba wasun su a kasa wasu a babura suna nuna murnar su.

Lokacin da su ka isa gidan su Barista

Wannan ya biyo bayan yajin aikin kwanaki uku da masu baburan suka yi tun a farkon satin da muke ciki bisa ikrarin da suke yi akan wasu kudi da hukumar KAROTA ta ce su biya.

asuu news

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Rundunar sojin ruwa za ta kafa sansani a Kebbi

Rundunar sojin ruwan Najeriya ta bayyana aniyar kafa sansaninta...

Za afara rijistar masu zabe a Najeriya – INEC

Hukumar zaɓe ta INEC, ta ce, nan gaba cikin...

Ma’aikatan Jinya sun dakatar da yajin aiki a Najeriya

Ministan lafiya a Najeriya ya ce, ma'aikatan jinya da...

Izak ya na ɗaukar horo bayan ya dage sai ya koma Liverpool

Ɗanwasan gab ana Newcastle Alexander Isak na can yana...

Masu tsaigunta wa ƴan Bindiga ne ke haddasa kashe-kashe – Gwamnan Katsina

Gwamnatin jihar Katsina ta ce masu tsegunta wa ƴanbindiga...

Gwamnoni ku yi wa mutanen ƙauyika da karkara ayyuka – Tinubu

Shugaba Bola Tinubu, ya buƙaci gwamnonin ƙasar nan su...

Dino Melaye ya gudu daga PDP ya faɗa ADC

Tsohon ɗan jamalisar dattawa mai wakiltar Kogi ta Yamma,...

Isra’ila na zargin Canada da goyon bayan Hamas – Netanyahu

Isra'ila ta zargi Canada da taimaka wa Hamas bayan...

Rashin tallafin agaji ka iya dawo da Boko Haram a Najeriya – MDD

Hukumar Samar da Abinci ta Majalisar Dinkin Duniya ta...

Yin gini a kan hanyoyin ruwa ne ya janyo ambaliyar Maiduguri – NEMA

Hukumar bayar da agajin gaggawa da Najeriya NEMA ta...

Amnesty ta yi Allah wadai da tsare Sultan kan bidiyon lafiyar Tinubu

Ƙungiyar kare haƙƙin bil'adama ta Amnesty International ta yi...

Dalilin da ya sa na gana da Tinubu – Kofa

Ɗan majalisar tarayyar mai wakilitar Kiru da Bebeji daga...
X whatsapp