fidelitybank

Mu tashi tsaye wajen tunkarar tsaro a Najeriya -Ganduje

Date:

Gwamnan jihar Kano, Dr. Abdullahi Umar Ganduje, ya yi kira ga rundunar sojojin Najeriya da su tashi tsaye wajen tunkarar kalubalen rashin tsaro da ke addabar kasar, tare da kawar da masu aikata laifuka a kasar.

Gwamnan ya yabawa jami’an tsaro a kasar nan kan ayyukan sadaukar da kai da suke yi wajen wanzar da zaman lafiya a kasar, inda ya bukace su da su yi aiki tukuru da tabbatar da dunkulewar Nijeriya tare da tabbatar da tsaro.

Da ya ke jawabi a ranar Asabar a Kano, bayan ya ajiye fure a wajen taron tunawa da ranarĀ  sojojin kasar, Ganduje ya bayyana cewa, dangane da yadda ake baiwa jaruman da suka shude, jami’an tsaro a Najeriya za su dauki nauyin da ya rataya a wuyansu.

ā€œBabu shakka wannan rana ce da ya kamata mu rinka tunawa a kowace shekara. Ina taya masu shirya taron murna da suka shirya taron tsawon kwanaki bakwai da suka gabata kuma yau an kammala komai.

ā€œMuhimmancin wannan rana shi ne tunawa da wadanda suka yi yakin basasar Najeriya, domin ganin Najeriya ta kasance kasa daya. Babu shakka muna amfana daga abin da suka yi a baya domin haka ya na da kyau mu tuna da su.

ā€œHaka zalika idan aka yi la’akari da kalubalen tsaro da muke fama da shi a kasar nan, wannan rana na da matukar muhimmanci ta yadda jami’an tsaronmu za su dauki nauyin da ya rataya a wuyansu da gaske, ta yadda za mu ci gaba da wanzuwa a matsayin kasa daya na kawar da kanmu daga masu aikata laifuka a cikinmu,ā€ in ji Ganduje. .

Sauran wadanda suka halarci bikin tunawa da ranar sun hada da mai martaba Sarkin Kano, Alhaji Aminu Ado Bayero da manyan hafsoshin Soja da Sojojin Sama, na ruwa da NSCDC, da Kwamishinan ā€˜yan sanda.

Sauran su ne matan sojoji, kungiyoyin ma’aikatan soja da suka yi ritaya da iyalansu.

 

vanguard news paper

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Za mu ɗauki matakin hana sake faruwar kisan mutane – Gwamnatin Filato

Gwamnatin jihar Filato ta jaddada aniyarta ta ɗaukar mataki...

Babu barazanar tsaro a Abuja – Najeriya

Gwamnatin Tarayya ta ce, babu wata barazanar a babban...

Isra’ila za ta mayarwa da Iran martani duk da tsagaita wuta

Ministan tsaron Isra'ila, Katz ya bayyana cewa, ya ba...

Ba mu kai wa Isra’ila hari ba – Iran

Kafar watsa labarai ta Iran ta ruwaito gwamnatin ʙasar...

Duk da faduwar farashin mai NNPCL ya kara farashi

Kamfanin man fetur na Najeriya, NNPCL ya ʙara farashin...

Duk wasu ʙawayen Amurka za su ɗanɗanar kuɗarsu – Iran

Rundunar dakarun juyin juya halin Iran ta fitar da...

Iran ta mayar da martani kan sojojin Amurka dake Qatar

Kafofin yaɗa labaran Iran sun bayyana cewa ʙasar ta...

Faransa ba ta goyon bayan Amurka na kifer da gwamnatin Iran – Barrot

Ministan harkokin wajen Faransa ya ce, ʙasarsu ba ta...

Kotu a Kano ta ɗaure masu satar Yara

Babbar kotun jihar Kano da ke zamanta a Miller...

Ba wata hujja da Amurka za ta kai wa Iran hari – Rasha

An gudanar da tattaunawa tsakanin shugaban Rasha Vladimir Putin...

Tinubu ya miʙa saʙon ta’aziyya ga mutanen Kano da Kaduna da Borno

Shugaba Bola Tinubu ya yi Alla-wadai da kisan wasu...

Amurka ta tafka babban kuskure – Iran

Ministan harkokin wajen Iran, Abbas Araghchi ya yi Alla-wadai...
X whatsapp