fidelitybank

Ƴan ta’adda sun ƙona fasinjoji 42 a cikin mota a Sokoto inda 37 su ka rasu nan take

Date:

 

Rahotanni daga Jihar Sokoto sun baiyana cewa ƴan ta’adda sun ƙona wata motar fasinja ɗauke da mutum 42.

Rahotanni sun baiyana cewa mutum 37 sun ƙone ƙurmus, inda biyar kuma su ka tsira da raunuka daban-daban.

BBC Hausa ta rawaito cewa fasinjojin sun fito ne daga Ƙaramar Hukumar Sabon Birni da ke jihar domin yin ƙaura zuwa wasu yankunan Najeriya, saboda ta’azzarar ayyukan ƴan bindiga a inda suke.

Wasu shaidu sun cewa BBC Hausa cewa lamarin ya faru ne da misalin karfe 9 na safiyar ranar Litinin.

“Motar ɗauke da fasinjojin ta tashi daga Sabon Birni, ta yi tafiyar da bai fi kilomita shida ba zuwa kauyen Gidan Bawa inda wannan masifa ta afka mata,” kamar yadda waɗanda suka yi aikin ceton suka bayyana wa BBC.

Tuni dai aka yi jana’ziar mamatan in ji shaidu.

Wani ganau ya cewa BBC: “Lokacin da abin ya faru ina Sabon Birni aka kira ni aka shaida min. Daga cikin matafiyan ma har da wani ƙanin mahaifiyata da matarsa da ƴaƴansu huɗu.

“Cikin ƴaƴan Allah Ya yi wa biyu rasuwa. Lokacin da muka isa wajen da ya faru mun je mun iske mutane sun mutu, kuma a ƙalla mun ƙirga gawarwaki sun kai 25,” ya ce.

Ya ƙara da cewa akwai tsirarun mutane daga cikinsu da suka tsira.

Shi ma wani shaidan da ya buƙaci a sakaya sunansa ya ce “mutum 45 ne a cikin motar, amma bakwai ne suka tsira da rayukansu, su ma a yanzu haka suna cikin halin ha’ula’i.

“Babu maganar ma ka ga gawa a kammale, sai dai muka dinga haɗa ƙafafu da hannaye daban-daban aka yi musu jana’iza a tare.”

Ya ce shi yana tsaye a tasha ma lokacin da motar ta tashi. “Ƴan Union ne ma na tasha suka gaya mana adadin mutanen da motar ta tashi da su,” a cewarsa.

Yankin arewa maso yammacin Najeriya na ɗaya daga cikin yankunan da suka fi fama da matsalar tsaro a Najeriya, sai dai a lokuta da dama gwamnatocin yankin na cewa suna iya kokarinsu domin tabbatar da kare rayuka da dukiyoyin al’umarsu, abin da al’umar ke cewa ba sa gani a kasa.

nnn news

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Har yanzu ina LP kuma ni ne zan iya saita Najeriya – Datti

Datti Baba-Ahmed, tsohon dan takarar mataimakin shugaban kasa a...

APC ta zama buhun kusa ta gaza a Najeriya – Amaechi

Tsohon gwamnan jihar Ribas, Chibuike Amaechi ya bayyana jam'iyyar...

An fara samun takun saka tsakanin Turkiyya da Najeriya a kan kungiyar Gulen

Kungiyar kare hakkin musulmi, MURIC, ta bukaci shugaban kasar...

Arziƙin Najeriya ya ƙaru da kashi 3.13 a farkon 2025 – NBS

Tattalin arzikin Najeriya ya ƙaru da kashi 3.13 cikin...

Kamfanonin lantarki za su katse wutar lantarki saboda bashi

Kamfanonin samar da wutar lantarki, sun ce suna iya...

Yunwa na kara tsananta a arewa maso gabashin Najeriya – ICRC

Kungiyar agaji ta Red cross (ICRC) ta bayyana yadda...

Ba zan taba watsawa Tinubu kasa a ido ba – IBB

Ɗan tsohon shugaban kasa, Janar Ibrahim Badamasi Babangida, wato...

Natasha kar ki kuskura ki dawo aiki – Majalisa

Majalisar Dattijai ta buƙaci Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan ta dakatar...

Za a yi ruwan sama da iska mai ƙarfi a jihohi harda Kano – NiMET

Hukumar kula da yanayi ta Najeriya (NiMET) ta fitar...

Obi da El-Rufa’i za su koma jam’iyyar mu a hukumance – ADC

Sakataren yada labarai na rikon kwarya na jam’iyyar African...

Za mu tattauna da tarayyar Turai a kan Nukiliyarmu – Iran

Iran ta tabbatar cewa za ta gudanar da tattaunawa...

Mu na gargadin Isra’ila kan korar al’ummar Gaza daga yankin su – MDD

Hukumar kula da ayyukan jin-ƙai ta Majalisar Ɗinkin Duniya...
X whatsapp