fidelitybank

Ƴan bindiga sun sace mata biyu a jami’ar Tarayya ta Gusau

Date:

Ƴan bindiga sun sace ɗalibai mata biyu na jami’ar tarayya da ke Gusau a jihar Zamfara.

Rahotonni sun ce ‘yan fashin ɗauke da muggan makamai, sun sace ɗalibai mata guda biyu a ɗakunan kwanansu da ke wajen makarantar.

A wata sanarwa da rundunar ‘yan sandan jihar ta fitar, ta ambato kwamishinan ‘yan sandan jihar CP Kolo Yusuf na tabbatar wa da dangin ɗaliban da kuma hukumar makarantar cewa rundunar na ƙoƙari wajen kuɓutar da ɗaliban.

Sanarwar ta ce, rundunar ‘yan sandan ta samu labarin sace ɗaliban a ɗakunan kwanansu da ke a wajen makarantar.

Tun bayan samun labarin sace ɗaliban ne, rundunar ‘yan sandan ta ce ta tura jami’anta zuwa wajen da lamarin ya faru, to sai dai kafin zuwan jami’an tsaron ‘yan fashin sun tsere da ɗaliban, kamar yadda sanarwar ta bayyana.

Haka kuma sanarwar ta ce kwamishinan ‘yan sandan ya tura ƙarin jami’an tsaro domin kuɓutar da ɗaliban, tare da kama ‘yan fashin domin gurfanar da su a gaban shari’a.

Daga ƙarshe kwamishinan ‘yan sandan jihar ya yi kira ga al’umma da su ci gaba da bai wa jami’an tsaron haɗin kai domin samun nasarar kuɓutar da ɗaliban

latest news in nigeria today 2022 punch

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Da yuwar Sojojin mu za su shiga yaƙi don tallafa wa Isra’ila – Trump

Rundunar sojin Isra'ila IDF ta ce ta ƙaddamar da...

Isra’ila ta kai hari cibiyoyin ƙera nukiliyar Iran

Yayin da aka shiga rana ta shida na yaƙi...

Najeriya za ta kwashe ƴan ƙasarta dake zaune a Iran da Isra’ila

Gwamnatin tarayya ta ce, tana kammala shirye-shiryen gaggawa domin...

Makami mai Linzami ya faɗa kan cibiyar tattara bayanan sirrin Isra’ila

Kafar yaɗa labarai ta gwamnatin Iran ta ce, ƙasar...

Iran ta ƙaddamar da sabbin hare-haren makamai masu linzami kan Isra’ila

Rundunar sojin Isra'ila ta ce, Iran ta ƙaddamar da...

Isra’ila ta na da makaman nukiliya 90

Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu ya dade yana cewa Iran...

Kashe jagoran Iran Ayatullah shi ne kawo ƙarshen rikici – Isra’ila

Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu ya ce duk wani shiri...

Jerin sunayen masu Fashin Waya 51 da aka kama a Kano

Rundunar ƴansandan Kano, ta fitar da jerin sunayen Mutane...

Iran ta dakatar da tashin jirgi a ƙasarta

Hukumar kula da zirga-zirgar jiragen sama ta Iran ta...

Poland za ta kwashe dukkannin ƴan ƙasarta daga Isra’ila

Poland na shirin kwashe kusan ‘yan kasarta 200 daga...

Kisan Binuwai abun haushi ne bai kamata a ƙyale ba – Atiku

Atiku Abubakar ya yi Allah-wadai da Kisan Benue, tare...

Ƴan Bindiga sun ajiye makamai a Katsina

Wasu fitattun jagororin ƴanbindiga da suka addabi yankunan ƙaramar...
X whatsapp