fidelitybank

‘Ƴan APC za su karɓi kuɗin Tinubu kuma su ƙi zaɓar sa a 2023’

Date:

Babban Fasto na Cocin Divine Mercy, Olatobiloba Peters ya yi hasashen cewa ƴan jam’iya mai mulki ta APC za su ci kuɗin Bola Ahmed Tinubu ne kawai su kuma ko zabar sa.
Ya kuma gargaɗi Tinubun, mai neman tsayawa takarar shugaban ƙasa a 2023 da kada ya ci gaba da burinsa na zama shugaban ƙasa.
Fasto Peters ya ce ƴan jam’iyyar  APC, za su karɓi kuɗin Tinubu kawai kuma su ƙi kaɗa masa ƙuri’a.
Da yake zantawa da DAILY POST, limamin ya ce Ubangiji ne ya nuna masa cewa ‘yan APC za su yi amfani da kudin Tinubu su cicciɓa mataimakin shugaban kasa, Osinbajo ya zama shugaban kasa.
Tinubu, wanda ya sanar da shugaban kasa Muhammadu Buhari aniyarsa ta tsayawa takarar shugabancin kasar a 2023, ya ce matakin wani buri ne a gare shi tsawon rayuwarsa.
Jagoran jam’iyyar APC na Ƙasa ya ce yana ci gaba da tuntuɓar masu ruwa da tsaki a kan matakin da ya ɗauka na maye gurbin Buhari a 2023.
Sai dai Fasto Peters ya ce Ubangiji ya halicci Tinubu ne domin ya kafa sarakuna ba wai shi ya zama ba.
Limamin ya bukaci tsohon gwamnan jihar Legas ɗin da kada ya barnatar da kudinsa a kan kudirinsa na shugaban kasa.
Sai dai ya yi gargadin cewa ‘yan Najeriya za su yi nadama idan har Tinubu ya tilasta wa kan sa mulki ta hanyar magudi.

legit news.com

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Farfesa Jibril Aminu ya rasu ya na da shekaru 86

Allah ya yi wa Farfesa Jibril Aminu mai shekara...

Alhajin Najeriya ya rasu a tsayuwar Arfa

Wani Alhaji daga Najeriya ya rasu a filin Arfa...

Alhazai miliyan 1.673,230 ne ke gudanar da akin Hajji – GASTAT

Hukumar tattara alƙaluma ta Saudiyya (GASTAT) ta ce, Alhazai...

Isra’ila ta gano gawar ƴan ƙasarta

Rundunar sojin Isra'ila ta ce ta gano gawar ''yan...

Ma’aikatan wutar lantarki a Abuja sun fusata

Ma'aikatar kamfanin rarraba wutar lantarki na Abuja Electricity Distribution...

Ƴan Najeriya 147 da suka maƙale a Nijar sun dawo gida

Gwamnatin Najeriya ta tarɓi 'yan ƙasar 147 aka kwaso...

Alhazai Miliyan Ɗaya da Rabi ke tsayuwar Arfa

Dubun dubatar alhazai daga sassan duniya na hawan Arafa...

Sarkin Kano na 15 ya dakatar da yin hawan Sallah

Mai martaba Sarkin Kano na 15, Alhaji Aminu Ado...

Maniyacin jihar Kano da yake kokarin zama Alhaji ya rasu a Saudiyya

Daya daga cikin alhazan jihar Kano, Shu’aibu Jibrin, an...

Tinubu ya bayar da tallafin Biliyan Biyu da Tirela 20 na Shinkafa ga al’ummar Mokwa

Mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima ya ce, shugaban ƙasar...

Gwamna Adeleke na Osun ya gana da Tinubu

Gwamnan jihar Osun Ademola Adeleke ya kai ziyara ga...

An samu gawar mutane 7 a ambaliyar Neja

Rahotonni na cewa masu aikin ceto sun zaƙulo gawar...
X whatsapp