Ƴan sandan Pakistan sun shaida wa BBC cewa aƙalla mutum 20 ne suka rasu tare da jikkata sama da 50 sakamakon fashewar bam.
Lamarin ya faru ne a kusa da wani masallaci yayin da mutane suka taru don yin bikin tunawa da haihuwar Annabi Muhammad (SAW) ko kuma maulidi a yau Juma’a a yankin Balochistan.
Ƴan sanda sun yi zargin cewa harin na ƙunar-baƙin-wake ne a birnin Mastung.
Hukumomi sun saka dokar ta-ɓaci, yayin da ake ci gaba da kai waɗanda suka jikkata asibitoci biyu mafiya kusa.
Bidiyon da aka yaɗa a shafukan sada zumunta ya nuna yadda masu bayar da agajin gaggawa da jama’ar yankin ke aikin ceto.
Zuwa yanzu babu wata ƙungiya da ta ɗauki alhakin kai harin.