Nathan Tella ya ce “Burinsa zai cika” yayin da yake shirin buga wa Najeriya wasa a gasar neman gurbin shiga gasar cin kofin duniya ta Fifa ta 2026 a mako mai zuwa.
An sanya sunan ɗan wasan, mai shekara 24 da haihuwa, wanda ke wasa a ƙungiyar Bayer Leverkusen, cikin tawagar Super Eagles ta Najeriya da za ta kara da Lesotho da kuma Zimbabwe.
An haife shi a Lambeth, da ke ƙasar Ingila, amma ya cancanci buga wa Najeriya ta dalilin iyayensa, makomarsa ta kasa da kasa ta kasance batu mai mahimmanci tun lokacin da ya fara yin tasiri a ɓangaren matasa a Arsenal.
Tella ya shaida wa BBC cewa, “A kullum batuna wakiltar Najeriya ne.”
“Iyalina za su kasance cikin matukar farin ciki don ganin na cika wannan burin.
“Ina alfahari da asalina na ɗan Birtaniya da Najeriya kuma na yi sa’a da samun al’adu biyu. Tabbas mun haɗa al’adun ɓangarorin biyu, amma gidanmu cikkaken gidan ƴan Najeriya ne ta fannin abinci, da al’adu”
Tella ya kasance ɗaya daga cikin fitattun ƴan wasan ƙungiyar Burnley a kakar wasan da ta gabata yayin da Clarets suka samu gurbin komawa matakin gasar Firimiya, amma ya koma asalin ƙungiyarsa ta Southampton a ƙarshen kakar wasan.
Ɗan wasan gaban, wanda zai iya taka leda a gefe ko kuma ta tsakiya, ya bayar da gudunmawar ƙwallaye 22 a kakar wasan da ta gabata kuma ya koma Leverkusen a kan farashin fam miliyan 20 a watan Agusta.
Sabuwar ƙungiyarsa ba ta yi rashin nasara ba a gasar Bundesliga na Jamus bayan wasanni 10 kuma ana tunanin bajintarsa za ta ƙara wa tawagar Super Eagles ƙarfi a ɓangaren ‘yan wasan gaba.
Bayan rashin halartar gasar cin kofin duniya da za a yi a Qatar a shekarar 2022, ‘yan Afirkan ta Yamman sun fara yaƙin neman gurbin shiga gasar ta 2026 inda za su fafata da Lesotho da Zimbabwe a ranakun 16 da 19 ga watan Nuwamba.
Ana sa ran Najeriya za ta tsallake daga rukunin C a saman takwarorinta na Afirka ta Kudu da Benin, inda ƙasashen da suka yi nasara a rukunin za su tabbatar da samun gurbi a gasar da za a yi a ƙasashen Canada da Mexico da kuma Amurka bayan da aka ƙara yawan ƙasashe daga 32 zuwa 48.