Dan takarar jam’iyyar All Progressives Congress, APC a zaben kananan hukumomin jihar Jigawa mai zuwa na karamar hukumar Kirikasamma Yahuza Umar Labbo ya rasu.
Shugaban jam’iyyar na jihar Aminu Gumel ne ya tabbatar da rasuwarsa.
Ya rasu yana da shekaru 55 bayan gajeriyar rashin lafiya, ya bar mata uku da ‘ya’ya goma sha biyar.
Gwamna Umar Namadi ya jajantawa ‘yan uwa da daukacin al’ummar musulmi.
Ya kuma yi addu’ar Allah ya jikan shi da rahama ya kuma baiwa iyalai hakurin jure rashin.
Wannan na zuwa ne kwanaki masu zuwa a gudanar da zaben kananan hukumomi a Jigawa