Dan majalisar dokokin jihar Kano mai wakiltar mazabar Dawakin Kudu, Mu’azzam El-Yakuba, ya fice daga jam’iyyar New Nigeria People’s Party (NNPP) zuwa jam’iyyar All Progressives Congress (APC) mai mulki.
A farkon watan nan ne dan majalisar tare da wasu mambobin jam’iyyar PDP tara suka sauya sheka zuwa jam’iyyar NNPP.
Sai dai a ranar Juma’a dan majalisar ya mika wasikar sauya sheka zuwa majalisar dokokin jihar.