fidelitybank

Ɗan majalisar Amurka ya janyo wa kansa jagwal bisa alaƙa da ɗan Najeriya

Date:

Wani dan majalisar dokokin Amurka na jam’iyyar Republican na fuskantar hadarin korarsa daga majalisar, saboda karya da ya yi kan wani tallafin kudi na siyasa da ke da alaka da wani attajiri dan Najeriya.

Masu taimaka wa alkali yanke hukunci, na tarayya sun gano cewa Jeff Fortenberry, dan majalisar wakilai daga Nebraska, ya yi wa jami’an hukumar binciken manyan laifuka ta Amurka, FBI, karya kan karbar tallafin da ya saba wa doka, daga attajiri Gilbert Chagoury, wani hamshakin attajirin dan kasuwa dan Najeriya.

Yanzu dai a sakamakon wannan bincike da masu taimaka wa alkalin suka yi inda suka gano cewa dan majalisa Jeff Fortenberry ya shirga wa jami’an na FBI, masu binciken laifuka karya game da kudin tallafin na siyasa da attajirin dan Najeriya ya ba shi, zai iya rasa kujerarsa ta wakilci a majalisar.

Sannan kuma bayan rasa kujerar, zai iya fuskantar daurin shekara 15 a gidan maza, a bisa laifuka uku.

A bisa dokar Amurka, haramun ne ga ‘yan kasashen waje su bayar da wani tallafi na siyasa, to amma kuma Mista Chagoury, mai shekara 75, ya dade yana yin hakan.

A shekara ta 2019, gwamnatin Amurka ta ci tararsa dala miliyan 1.8, kuma aka gudanar da bincike a kan wasu daga cikin wadanda suka ci moriyar tallafin nasa.

A shekara ta 2016, ne ya bayar da tallafin da ya saba doka na dala dubu 30 ga dan majalisa Fortenberry, amma ta hannun wasu masu bayar da tallafi a yayin wani taro a Los Angeles

Ana sa ran yanke masa hukunci a ranar 28 ga watan Yuni, amma kuma ya ce zai dukaka kara. A cewar BBC.

legitnews.com

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Duk wasu ƙawayen Amurka za su ɗanɗanar kuɗarsu – Iran

Rundunar dakarun juyin juya halin Iran ta fitar da...

Iran ta mayar da martani kan sojojin Amurka dake Qatar

Kafofin yaɗa labaran Iran sun bayyana cewa ƙasar ta...

Faransa ba ta goyon bayan Amurka na kifer da gwamnatin Iran – Barrot

Ministan harkokin wajen Faransa ya ce, ƙasarsu ba ta...

Kotu a Kano ta ɗaure masu satar Yara

Babbar kotun jihar Kano da ke zamanta a Miller...

Ba wata hujja da Amurka za ta kai wa Iran hari – Rasha

An gudanar da tattaunawa tsakanin shugaban Rasha Vladimir Putin...

Tinubu ya miƙa saƙon ta’aziyya ga mutanen Kano da Kaduna da Borno

Shugaba Bola Tinubu ya yi Alla-wadai da kisan wasu...

Amurka ta tafka babban kuskure – Iran

Ministan harkokin wajen Iran, Abbas Araghchi ya yi Alla-wadai...

Trump ya yaudari Amurkawa da Iran – Aragachi

Ministan harkokin wajen Iran, Abbas Araghchi ya bayyana cewa...

Sai an hukunta Mutanen da suka kashe ƴan ɗaurin aure – Uba Sani

Gwamnan jihar Kaduna Uba Sani ya yi Alla-wadai da...

An fara binciken fashewar wani abu da ya kashe mutane 5 da jikkata da dama a Kano

Wani abin fashewa da ake tunanin bom ne ya...

An samu fashewar wani abu a kamfanin ƴan Chana a Kano

An samu fashewar wani abu a Kamfanin Ƙarfe na...

Ma’aikacin kamfani ya kashe abokin aikinsa a Kano

Rahoton da ke yawo a kafafen sada zumunta ya...
X whatsapp