Mawallafin mujallar Ovation International kuma dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar People’s Democratic Party (PDP), Dele Momodu, ya samu nasarar zartas da tsarin tantance shugaban kasa na jam’iyyar.
Daily Independent ta tattaro cewa, kwamitin tantance ƴan takarar shugaban kasa da Sanata David Mark ya jagoranta ya gabatar da takardar shaidar amincewa ga masu neman takarar da aka yi nasarar wanke su bayan an kammala tantance masu neman shugabancin kasar su 17 a ranar Juma’a, 29 ga watan Mayu.
Da yake zantawa da kafar sadarwarsa ta sada zumunta, Dele Momodu, ya ce, ya yi matukar farin ciki da samun takardar shedar tsayawa takara a jam’iyyar gabanin babban zaben 2023.