Dan wasan baya na kasar Faransa,Axel Disasi, ya koma Chelsea daga Monaco kan kwantiragin shekara shida akan Yuro miliyan 45 (£38.57m).
Disasi, mai shekaru 25, ya koma kungiyar ta Stamford Bridge bayan Wesley Fofana ya samu mummunan rauni a gwiwa.
Ya buga dukkan wasanni 38 a gasar Ligue 1 ta Monaco a kakar wasan da ta wuce.
Disasi ya buga wa Faransa wasa sau hudu, ciki har da wanda ya shigo daga baya a wasan ƙarshe na cin Kofin Duniya na 2022 da Faransa ta fafata da Argentina, kuma ya buga wa Monaco wasanni 129 bayan ya koma daga Stade de Reims a watan Agustan 2020.
Dan wasan ya zama na shida da Chelsea ta saya a bazara bayan sayen Christopher Nkunku da Nicolas Jackson da Lesley Ugochukwu da Angelo Gabriel da kuma Diego Moreira, yayin da sabon koci Mauricio Pochettino ke ci gaba da sanya tambarinsa a kan kungiyar.
A halin da ake ciki, Chelsea ta amince da farashi mai tsaron gida Robert Sanchez da Brighton, yayin da Brighton ta cigaba da kin amincewa da tayin da Chelsea ke yi kan dan wasan tsakiya Moises Caicedo.
Chelsea ta kammala wasannin share fage a ranar Lahadi da ta yi kunnen doki ci 1-1 da Borussia Dortmund a birnin Chicago – wanda ya kawo karshen rangadin da suka yi a Amurka ba tare da an doke ta ba.
Kuma yanzu hankali ya koma kan wasansu na farko na gasar Premier na 2023/24 a gida da Liverpool ranar 13 ga watan Agusta.