fidelitybank

Ɗalibin da a kai garkuwa da shi ya ƙi dawowa gida, ya ce ya fi jin daɗin zama da ƴan ta’addan

Date:

 

 

 

Ɗalibi ɗaya tilo da ya yi saura a hannun ƴan fashin dajin da su ka yi garkuwa da ɗalibai 121 na Makarantar Bethel Baptist High School a Jihar Kaduna ya ce ya fi jin daɗin zama a hannun ƴan ta’addan.

A tuna cewa a ranar 5 ga watan Yulin 2021 ne ƴan ta’addan su ka kutsa kai cikin makarantar da ke kan titin Kaduna-Kachia, a ƙauyen Damishi, da ke Ƙaramar Hukumar Chikun su ka yi awon-gaba da ɗaliban.

Jaridar Vanguard ta rawaito cewa Shugaban Ƙungiyar Kiristoci ta Ƙasa, CAN, reshen Jihar Kaduna, Rabaran Joseph John Hayab ne ya baiyana hakan.

A cewar sa “ɗalibi ɗaya da ya yi saura a hannun ƴan fashin daji, wanda shi ne mafi kankanta a cikin su, ya ce ba zai dawo gida ba.

“Ya ce shi zai ci gaba da zama da ƴan fashin dajin. Wannan abin al’ajabi ne ga ɗaukacin ƴan ɗariƙar Baptist da ma CAN baki ɗaya.

“An ce wai ƴan ta’addan na bashi kyautar kayaiyaki ne duk sanda su ka je su ka kai hari su ka dawo, shi ya sa ya ki yadda ya dawo gida.

“Ina ganin wayo su ka yi wa yaron su ka riƙa bashi kayan daɗi domin su yaudari zuciyarsa ya ji baya son komawa gida. An ce wai yaron ya ma gaya musu cewa shi ba ya son komawa wajen iyayen sa saboda wai dama dukan sa a ke yi gida idan yai laifi.

Hayab ya ƙara da cewa shima mutumin da ya saba kai wa ƴan ta’addan kuɗin fansa sun riƙe shi bayan da ya ke kai kuɗin fansar shi wannan yaron da ya ce ba zai dawo ba.

“Gaba ɗaya ma lamarin ya jefa mu cikin ruɗani. Shi mutumin da ya saba kai musu kuɗaɗen fansa, ko me ya faru?, ya je kai kuɗin fansar shi wannan yaron, ƴan ta’addan sun riƙe shi.

“To gaba ɗaya lamarin ya ɗauki wani sako na daban. Mu na dai roƙon Ubangiji ya kawo mana ɗauki,” in ji Hayab.

Ya kuma yi kira ga mahukunta da su dage su ƙwato yaron nan da ga hannun ƴan ta’adda da ma sauran mutanen da a ka yi garkuwa da su.

 

nigerianews.com

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Farfesa Jibril Aminu ya rasu ya na da shekaru 86

Allah ya yi wa Farfesa Jibril Aminu mai shekara...

Alhajin Najeriya ya rasu a tsayuwar Arfa

Wani Alhaji daga Najeriya ya rasu a filin Arfa...

Alhazai miliyan 1.673,230 ne ke gudanar da akin Hajji – GASTAT

Hukumar tattara alƙaluma ta Saudiyya (GASTAT) ta ce, Alhazai...

Isra’ila ta gano gawar ƴan ƙasarta

Rundunar sojin Isra'ila ta ce ta gano gawar ''yan...

Ma’aikatan wutar lantarki a Abuja sun fusata

Ma'aikatar kamfanin rarraba wutar lantarki na Abuja Electricity Distribution...

Ƴan Najeriya 147 da suka maƙale a Nijar sun dawo gida

Gwamnatin Najeriya ta tarɓi 'yan ƙasar 147 aka kwaso...

Alhazai Miliyan Ɗaya da Rabi ke tsayuwar Arfa

Dubun dubatar alhazai daga sassan duniya na hawan Arafa...

Sarkin Kano na 15 ya dakatar da yin hawan Sallah

Mai martaba Sarkin Kano na 15, Alhaji Aminu Ado...

Maniyacin jihar Kano da yake kokarin zama Alhaji ya rasu a Saudiyya

Daya daga cikin alhazan jihar Kano, Shu’aibu Jibrin, an...

Tinubu ya bayar da tallafin Biliyan Biyu da Tirela 20 na Shinkafa ga al’ummar Mokwa

Mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima ya ce, shugaban ƙasar...

Gwamna Adeleke na Osun ya gana da Tinubu

Gwamnan jihar Osun Ademola Adeleke ya kai ziyara ga...

An samu gawar mutane 7 a ambaliyar Neja

Rahotonni na cewa masu aikin ceto sun zaƙulo gawar...
X whatsapp