Harabar jami’ar Obafemi Awolowo, OAU, Ile-Ife, a ranar Laraba ta fuskanci zanga-zangar dalibai.
Zanga-zangar daliban ta biyo bayan kashe Okolie Arinze, wani dalibai mai digiri ajin 500 a fannin Injiniya a makarantar da yammacin ranar Litinin.
DAILY POST ta tattaro cewa daliban da suka yi zanga-zangar sun mamaye ginin kungiyar daliban, inda suka rufe shi.
Arinze, bayan an azabtar da shi bisa zargin satar wayar hannu a dakin taro na Awo dake jami’ar, an kawo gawarsa a cibiyar bada agajin gaggawa ta asibitin koyarwa na jami’ar Obafemi Awolowo dake Ile-Ife a ranar Talata.
A nata martanin hukumar jami’ar ta yi Allah wadai da lamarin.
A cikin wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na Jami’ar Abiodun Olanrewaju ya fitar, makarantar ta bayyana cewa, mataimakin shugaban jami’ar Farfesa Adebayo Simeon Bamire, ya kafa wani kwamiti domin bankado al’amuran da suka haddasa faruwar lamarin.
Sanarwar ta kara da cewa, ” Matakin da ‘yan kungiyar suka dauka, kasancewar ya saba wa dokar kasa da na jami’ar, an kai rahoto ga ‘yan sanda da suka fara bincike.”
A halin da ake ciki kuma, wata sanarwa mai dauke da sa hannun dukkan shugabannin tsangayar fasaha ta nuna cewa za a gudanar da zanga-zangar lumana don bayyana kokensu da kuma hukunta duk bangarorin da abin ya shafa.