Tsohon Shugaban Amurka Donald Trump, ya zargi sashen shari’ar ƙasar da ƙoƙarin farfaɗo da matacciyar tuhumar da ake masa kan ta ɗa hargitsi a zaɓen shekarar 2020.
Zargin na da alaƙa ƙoƙarin da Trump ya yi na juya sakamakon zaɓen da Shugaba Joe Biden ya yi nasara.
Wakilin BBC ya ce abin da kamar wuya gurfanar da Trump gaban shari’a kafin masu kaɗa ƙuri’a su yi zaɓe na watan Nuwamba mai zuwa.
Tun da fari an dai buƙaci wa lauyoyin gwamnati yin sauye-sauye kan tuhumar, bayan Kotun Ƙolin Amurka ta ce tsohon shugaban na da rigar kariya.