Wata yarinya ‘yar shekara 16 mai suna Sadiya Usman, ta rataye kanta a kauyen Garin Dauru da ke karamar hukumar Warawa a jihar Kano bisa zargin auren dole.
Kakakin Rundunar ’Yan sandan Jihar Kano, SP Abdullahi Haruna Kiyawa ya tabbatar wa DAILY POST faruwar lamarin.
A cewarsa “’yan sanda a ranar 01/08/2022 da misalin karfe 3:00 sun samu kiran waya daga Hakimin kauyen Garin Dauru da ke karamar hukumar Warawa cewa wata yarinya ta rataye kanta a dakinta”.
Ya ce, bayan samun rahoton ne aka tattaro tawagar ‘yan sanda zuwa wurin, inda suka gano cewa yarinyar ta yi amfani da nadenta da turmi na katako wajen rataye kanta.


