Rundunar ƴansandan jihar Kaduna ta ce, jami’an ta sun samu nasarar kama wani ‘ƙasurgumin ɗanbindiga’ a jihar da ke arewa maso yammacin Najeriya.
Tashar Channels mai zaman kanta ta ruwaito ƴansandan suna cewa sun kama ɗanbindigar mai suna Mati Bagio ne bayan kimanin shekara 11 suna nemansa ruwa a jallo.
Kakakin rundunar, Mansir Hassan ya ce Bagio mai kimanin shekara 34 ya daɗe yana addabar yankunan Giwa da Hunkuyi a Kaduna, da Faskari da Dandume da Funtua a jihar Katsina.
“Mun kama shi ne a ranar 18 ga watn Yulin tare da makamai da dama irin su alburusai da bindiga ƙirar AK-47 da sauran su.”